An kama matasa kan sharhi a Facebook
A Jamhuriyar Nijar an cafke wasu matasa masu dama na bangaren ’yan adawa bisa zargin yin amfani da kafafen sada zumunta don ta da tarzoma.Da farko dai an kama matasan masu yawa aka kuma sanya su a kurkuku,kafin daga bisani a sake su.Sai dai kuma har yanzu akwai mutane 10 da ke tsare, a gidan […]
A Jamhuriyar Nijar an cafke wasu matasa masu dama na bangaren ’yan adawa bisa zargin yin amfani da kafafen sada zumunta don ta da tarzoma.
Da farko dai an kama matasan masu yawa aka kuma sanya su a kurkuku,kafin daga bisani a sake su.
Sai dai kuma har yanzu akwai mutane 10 da ke tsare, a gidan yarin, kamar yadda BBC ta bayyana.
Ana dai zargin matasan ne da yada wasu bayanai da ka “iya haddasa fitina a cikin kasa” ta hanyar shafin sada zumunta na Whatsapp.
Sai dai shugabannin matasa magoya bayan jam’iyyar Moden Lumana sun yi watsi da zargin suna cewa bi-tada-kullin siyasa ne.
Hamayya dai tana kara kamari tsakanin jam’iyya mai mulki ta PNDS da bangaren adawa musamman jam’iyyar Moden Lumana, tun bayan zaben shugaban kasar da Mahamadou Issoufou ya lashe.
A ranar Talata ne Kotun daukaka kara a kasar, ta ba da belin tsohon Shugaban Majalisar Dokoki kuma dan takarar shugabancin kasar, Hama Amadou wanda yake tsare a gidan yari tun watan Nuwamban bara. Kodayake, an bayar da belinsa ne lokacin da yake karbar magani daga wani asibiti a birnin Paris da ke kasar Faransa