An kama matasa masu garkuwa da mutane a Kalaba

Dubun wani matashi mai suna bincent Ibor ta cika. Ya kware wajen kitsawa tare da kama mutane ana garkuwa da su domin karbar kudin fansa a Jihar Kurosriba da kewaye. Matashin dai da ’yan kungiyarsa sun fada komar rundunar ’yan sandan jihar. Matashin wanda dan asalin dan karamar Hukumar Akamkpa ne, ya shaida wa ’yan […]

An kama matasa masu garkuwa da mutane a Kalaba
An kama matasa masu garkuwa da mutane a Kalaba

Dubun wani matashi mai suna bincent Ibor ta cika. Ya kware wajen kitsawa tare da kama mutane ana garkuwa da su domin karbar kudin fansa a Jihar Kurosriba da kewaye. Matashin dai da ’yan kungiyarsa sun fada komar rundunar ’yan sandan jihar.

Matashin wanda dan asalin dan karamar Hukumar Akamkpa ne, ya shaida wa ’yan sanda a binciken da suka masa cewa tabbas ya karbi kudi Naira milyan 3 da rabi.
Ibor, dan shekara 25 da haihuwa, shi da abokansa, Justice Ajodo, mai dan shekara 21 da haihuwa sai kuma Stanley Obi dan shekara 20 da haihuwa da ya zarge su da sane suka sanya shi cikin harkar kama mutane ana garkuwa da su.
Da yake yi wa Aminiya karin haske game da yadda aka yi ya fada aikin kama mutane ana garkuwa da su don karbar kudin fansa matashi Ibor ya ce: “Wadannan da ka gani aka kama mu tare, su ne suka tsoma ni cikin harkar lokacin da suka gayyace ni walimar cika murnar zagayowar ranar haihuwar wani abokinmu, suka ce ga irin harkar da suke yi kuma idan ban ba su hadin kai ba za su halaka ni; shi ya sa na yanke shawarar ba bori kai ya hau.” Inji shi.
DSP Hogan Bassey, mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Kurosriba ya tabbatar wa wannan jarida cewa, wadanda aka kama su ne suka kama wani basarake mai suna Cif Samuel Onyeka, a unguwar Ikot-Ishie, birnin Kalaba, har sai da aka biya su kudin fansa tukuna suka sako shi da kuma shugaban Cocin Winners da ke Kalaba. Bayan namijin kokari da jami’ansa na sashen hana aikata miyagun laifuka suka kwato shi tukuna, duk da kudin fansar da suka karba. Nana ba da jimawa ba, ya ce da zarar sun gama bincikensu za a kai su kotu.