An kama matasa sun daura wa kansu aure a kan sadakin N3,000 a Bauchi
Daga cikin matasan da suka shiga hannu, akwai budurwa daya da ta yi wa amarya Uwar daki.
Sauran sun hada da wani abokin ango da ya zamo waliyyyin amarya da daya daga cikinsu kuma ya zamo limamin da ya daura auren.
Wasu matasa sun shirya tare da daura wa abokinsu aure da budurwarsa mai shekara 18 a a bisa sadaki Naira dubu uku, lamarin da ya zamo alakakai a Jihar Bauchi.
Kwana 14 bayan daurin auren ne gwamnati ta cika hannu da angon da aka daura wa auren mai suna Muhammad Chindo tare da amaryar tasa mai suna Kamila, wadanda mazaunan unguwar Mahaukata ne da ke cikin garin Bauchi, tare da abokansu mutum 8.
Gwamnati ta cika hannu da matasan su 10 ne bayan da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammad ya bayar da umarni a damko su duk inda suke, domin su girbi abin da suka shuka.
Da yake bayyana yadda ya kamo angon da amaryar da sauran abokansu ’yan daurin auren, Shugaban kungiyar ’Yan Sintiri na Jihar Bauchi, Alhaji Umaru Shayi, ya ce, sai da aka shafe kwana biyar bayan umarnin gwamnan sannan aka samu kamo mutum 10 a cikin matasan.
Yadda aka daura auren
Umaru Shayi, ya ce daga cikin matasan da suka shiga hannu, akwai budurwa daya da ta yi wa amarya Uwar daki.
Sauran sun hada da wani abokin ango da ya zamo waliyyyin amarya da daya daga cikinsu kuma ya zamo limamin da ya daura auren.
Sauran abokansu kuma su suka zamo shaidun daurin auren.
Ya yi wadannan bayani ne lokaci da ya gabatar matasan a gaban mai dakin Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Aishatu Bala Mohammed Abdulkadir, wacce ita ce Shugaban Kwamitin Yaki da Cin Zarafin Jinsi na Jihar.
Bayan haka ne matar gwamnan ta kira taron gaggawa na manema labarai da sarakunan gargajiya, inda ta nuna damuwa game da yadda irin wadannan matsalolin ke faruwa.
Umaru Shayi ya ce, an kama shaidun da suka halarci daurin auren, limamin daya daura auren ba bisa ka’ida ba da kuma yarinyar da aka aurar da mijin da ya aure ta.
A yayin da yake magana, Kwamandan Hisba na jihar, Mohammed Mohammed Bununu, ya ayyana auren a matsayin haramtacce, yana mai cewa mahaifin amaryar ya musanta sanin wannan mataki.
Yace bayyana cewa, a shari’ar Musulunci ba a yin aure sai da Sadaki kuma da yardar mahaifin yarinya, saboda haka wannan aure batacce ne.
Bununu ya ce jihar da ke aiwatar da shari’ar Musulunci ba za ta amince da irin wannan aure ya ci gaba ba, yana mai gargadin iyalai da su sake farfado da dabi’un Musulunci a gidajensu.
Uwargidan gwamnan ta yi Allah wadai da wannan mummunar dabi’a, inda ta kara da yin nasiha da kuma fada sosai tare da addu’ar Allah Ya sa hanyar shiriya matasan ke nan.
Sai ta yi kira ga iyaye da su sake sadaukar da kansu wajen sauke nauyin kula da ’ya’yansu da tarbiyyar su yadda ya kamata. kuma ta roki iyaye su rika lura da rayuwar ‘ya’yensu da gyaran tarbiyya ta hanyar sanya ido a kan su.
Ta kuma bukaci sarakuna da malaman addini da ’yan jarida su ci gaba da kokarin wayar da kan jama’a game da gyara halin matasa.
Yaya za a yi da yaran?
Wakilan Kwamitin Yaki da Cin Zarafin Jinsi da wasu iyayen yaran sun shafe sama da sa’o’i biyar suna tattaunawa kan abin da ya kamata a yi da yaran da kuma auren da suka yi ba bisa ka’ida ba.
Wasu mahalarta taron sun shaida wa wakilin Aminiya cewa yayin da wasu ke gani ya kamata gwamnati ta tallafa musu a gyara auren, wadansu kuwa na ganin yaran sun riga sun yi ganganci kuma ya kamata a hukunta su domin ya zamo darasi ga na baya.
A karshe bayan tattaunawar, an yanke shawarar mika lamarin ga rundunar ’yan sandan Jihar Bauchi don gudanar da bincike mai zurfi da nufin daukar matakai na Shari’a.
Kwamitin ya jaddada ci gaba da jajircewarsa wajen kare dabi’un iyali, inganta halayyar zamantakewa tsakanin matasa, da kuma tabbatar da cewa an bi hanyoyin shari’a a duk wani lamari da ya shafi walwalar matasa.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Bauchi, Nafiu Habib ya ce rundunar tana gudanar da bincike a kan lamarin. Ya bayyana cewa an bayar da belin yaro guda ga iyayensa saboda yana da jarrabawa a makaranta, bisa sharadin kullum zai kai kansa wurin ’yan sanda.
A cewarsa, bayan sun kammala bincike za su mika matasan ga Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar don daukar matakan da suka dace, saboda al’amarin aure yana da alaka da addini, kuma hukumar ke da hukurumin yin abin da ya kamata a kai.
Uban ango ya nemi a gyra auren
A hirarsa da da manema labarai, wani uban angon da aka daura wa auren, ya roki uwargidan Gwamna Bauchi ta sanya baki don a gyara auren bisa tsari na Shari’ar Musulunci maimakon a kai su gidan gyaran hali.
Mahaifin angon, Malam Abdullahi Muhammad Dumi, ya bayyana cewa, “gyara auren shi zai fi maimakon a ce za a kai su gidan gyaran hali saboda gudun kada su hadu da wadansu masu aikata laifin.”
Malam Abdullahi wanda shi ne mahaifin daya daga cikin matasan da ake tsare da su, ya bayyana cewa an kama yaronsa ne a gidansa cikin dare, kimain kwana takwas da suka wuce saboda ya halarci daurin auren mai cike da rudani, a matsayinsa na aboki kuma dan unguwa da suka taso tare da angon.
Shi ma ya roki uwargidan gwamnan ta taimaka ta sa baki a bayar da belin su kuma ta bayar da sadakin da ya dace don a gyara auren tsakanin Mohammed Chindo dan kimanin shekara 25 da Kamila Shehu ’yar kimanin shekara 18.
Ya kuma ya roki ta shiga cikin lamarin sauran a daura musu aure da ’yan matan da suke so, saboda a cewarsa, akasarin matasan da aka kama suna da budurwa kuma sun isa aure, amma talauci ya hana. Don haka yake zargin wannan dalili shi ya sanya matasan suka fito da sabon salon kulla aure tsakaninsu da wanda suke so ta kowane hali.
Malam Abdullahi ya ce kai yaran gidan yari yana da hadari, don haka ya yi kira ga uwargidan gwamnan ta bullo da tsarin auren gata kamar yadda ake yi a wasu jihohu, ta hanyar tallafin gwamnati don taimaka wa yaran da iyayensu.
Iyayen sun ce gyara auren zai sa yaran da iyayensu su kara samun nutsuwa da tsayar da hankalinsu wuri guda.
Jami’an Hukumar Hisbah a Hukumar Shariar Musulunci ta Jihar Bauchi sun bayyana cewa wannan batu ne mai sauki da za su iya gyarawa, saboda ba sa son a rika kai matasa gidan gyaran yari ko ofishin ’yan sanda saboda kada su dauki miyagun halayen da suka fi nasu a can.