An kama matasan da ake zargi da fashi da satar ababen hawa

’Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wadansu matasa shida da suke zargin sun kware wajen fashi da makami da satar babura da motoci a jihar. Kwamashinan ’Yan sandan Jihar, Mista Rasheed Olatunji Akintunde ya gabatar da wadanda ake zargi da fashin da barayin ababen hawan ga ’yan jarida a ranar Litinin din makon jiya, […]

An kama matasan da ake zargi da fashi da satar ababen hawa

’Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama wadansu matasa shida da suke zargin sun kware wajen fashi da makami da satar babura da motoci a jihar.

Kwamashinan ’Yan sandan Jihar, Mista Rasheed Olatunji Akintunde ya gabatar da wadanda ake zargi da fashin da barayin ababen hawan ga ’yan jarida a ranar Litinin din makon jiya, dukansu matasa ne masu karancin shekaru.

Wakilummu ya samu jin ta bakin wadanda ake zargin a gaban ’yan sandan, inda daya daga cikinsu mai suna Usman Mai’unguwa Gide da ke kauyen Magantara diya a karamar Hukumar Garki da ke jihar, inda ya ce an kama shi ne ana zarginsa da laifin fashi da makami amma bai aikata hakan ba, ya ce ya amsa ne saboda ya sha bakar wahala a wajen ’yan sandan lokacin da suke gudanar da bincike a kansa. 

Usman ya ce sau daya ya taba satar awaki 6 amma daga su ya tuba ya daina sata. Ya ce saboda kawai ana son a bata wa mahaifinsa suna ne aka ce yana cikin barayin da ake zargi sun je gidan wani mai kudi a kauyan Kwalan sun yi fashi da makami, amma shi ba ya cikinsu.

Ya ce kayan da aka kama shi da su irinsu kotar magirbi da kwari da baka da kibiyoyi gadonsu ya yi a wajen kakansa kuma yana amfani da su ne wajen kare kansa amma bai taba yin fashi da makami ba. 

Abokinsa da ake zargin tare suke yin fashin mai suna Sirajo Audu Limawa da ke kauyen Kwalam a karamar Hukumar Taura mai shekara 40, ya ce ba su aikata laifin da ake zarginsu da shi ba na yin fashi da makami, sharri aka yi musu saboda an gan su a ranar a cikin gari sun je sayayya, sai aka ce wai su ne suka yi fashin.

Sirajo Audu ya nuna damuwa game da halin da iyalansa za su shiga kan kazafin da ya ce an yi masa wai ya yi fashi da makami.

Shi kuwa Idris Hassan Gwale da Sadik Sani Gwale dukansu daga Jihar Kano ana tuhumasu ne da laifin satar babura suna kaiwa Kano su sayar. Kuma sun ce sun jima suna zuwa Jigawa suna satar babura kuma in sun sace ana ba su Naira dubu goma ne a kan duk babur din da suka kai Kano. 

Sun ce suna satar baburan ne a bakin bankuna idan suka ga masu su shagalta, inda suke amfani da mabudan da ake kira master key su dauke baburan kuma suna da uban gida a Kano da suke kai masa.

Sun ce dukansu dalibai ne a Makarantar Sakandiren Gwale da ke birnin Kano.

Su kuwa Abdulkadir Mukhtar Yakasai mai shekara 22 da Usman Ahmed mai shekara 22 daga karamar Hukumar Gumel ana tuhumarsu ne da hada baki suna satar motoci.

Abdulkadir Mukhtar ya ce suna yin amfani ne da mabudan Honda da Toyota da suke da saukin budewa su sace su.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, SP Audu Jinjiri ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu domin a yi musu hukunci.