An kama matashi bisa zargin fataucin mutane

Hukuma shigi da fice a Jihar Katsina ta kama wani matashi da ta yi zargin ya kware wajen fataucin mutane don tsallakawa da su zuwa kasashen ketare. Kwantarolan hukumar na jihar Mista Emmanuel N. Ogbumuo ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu matasa biyar […]

An kama matashi bisa zargin fataucin mutane
An kama matashi bisa zargin fataucin mutane

Hukuma shigi da fice a Jihar Katsina ta kama wani matashi da ta yi zargin ya kware wajen fataucin mutane don tsallakawa da su zuwa kasashen ketare. Kwantarolan hukumar na jihar Mista Emmanuel N. Ogbumuo ya bayyana wa manema labarai haka a lokacin da ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu matasa biyar da suka fito daga Jihar Edo, inda ya ce, jami’ansa sun kama matashin mai suna Muntari Hamidu a garin Kongolom ta karamar Hukumar Mai’aduwa ne a lokacin da yake kokarin tsallakawa da matasan da suka hada da ’yan mata uku da maza biyu, zuwa garin Maimujiya da ke Jamhuriyar Nijar a hanyarsu ta zuwa Libya da kasashen Turai.
Ya ce, matasan a karkashin jagorancin Atiba Esosa sun fito ne daga Jihar Edo da nufin tsallakawa Nijar da taimakon babban jagoransu Muntari, inda rana ta baci musu, bayan da Muntari a matsayinsa na direba ya dauke su a matsayin fasinjoji.
Muntari ya ce an taba kama shi sau daya a kan wannan laifi kuma a cewarsa tsautsayi da rashin sani ya sa ya dauke su.
Atiba Esosa mai shekara 23 da ke sana’ar gyaran takalma ya ce, talauci ne ya sa suka fito don zuwa neman kudi. Ya ce wani mutun ne (an sakaya sunansa) ya shirya komai wajen tahowarsu tun daga can Edo har zuwa Kano da nan inda aka kama su. Otiba ya ce duk garin da suka je za su tarar da motar da ke jiransu. Kuma har zuwarsu Kongolom suna magana da Muntari domin an ba su lambarsa.
Sauran wadanda aka kama suna kokarin tsallakawar sun hada da Jerry Igiewe mai shekara 25, sai Faith Idemude mai shekara 21 da Gift Osagwe da Joy Osifo dukkansu ’yan shekara 22.