An kama matashi da sassan jikin dan Adam
An cafke wani matashi da kokon kan dan Adam sabon yanka zai yi tsafi da shi.
An cafke wani matashi da sassan jikin dan Adam sabon yanka zai yi tsafi da su.
Jami’an rundunar tsaro ta Operation Harmony na Jihar Kwara sun damke matsafin ne a yayin binciken wata motar haya a hanyarAjase-Ipo zuwa Ilorin a ranar Litinin.
- Boko Haram ta kashe mutum 30 ta tashi sansanin soji a Borno
- An kara wa’adin hada layukan waya da NIN har zuwa karshen watan Yuni
Bude jakar matashin mai shekara 24 ke da wuya, sai jami’an suka ci karo da kai da hannu da wasu sassan jikin dan Adam sabbin yanka a ciki.
Da ganin asirinsu ya tonu, sai abokin matashin ya faki idon jami’an tsaron ya arce, inda suke ci gaba da bin sawunsa.
Mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya ce a yayin gudanar da bincike, matashin ya shaida musu cewa sassan jikin dan Adam da aka kama na wani mutum ne da suka kashe za su yi tsafi da shi.
“Masu bincike sun je sun dauko gawar da aka jefar zuwa asibiti domin gudanar da bincike,” inji shi.
Ya ce da zarar an kamama gudanar da bincike za gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya.