An kama matashi dauke harsasai 340 da ya boye a cikin buhun garin rogo
Suna cikin bincike suka yi arba da harsasai 340 da aka boye a cikin garin rogon.
’Yan sanda a Jihar Delta sun kama wani mutum mai suna Solomon Ebe da ake zarginsa da fashi da makami dauke da harsasai 340 da ya boye a cikin buhun garin rogo.
Mai magana da yawun rundunar ’yan jihar, DSP Bright Edafe ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Warri.
- An yi wa malami duka tare da tsare shi kan ladabtar da daliba
- Atletico Madrid ta lallasa Barcelona a gasar La Liga
Mista Edafe ya ce ’yan sanda a yankin Bomadi ne suka cafke mutumin da aka goyo a kan wani babur mai kafa uku da aka fi sani da Keke Napep, dauke da buhun garin rogon bayan sun kafa wani shingen binciken ababen hawa.
Ya ce a ranar Juma’a ce bayan ’yan sandan sun tare shi a kan titin Bomadi/Toama da ke Karamar Hukumar Bomadi, suka yanke shawarar binciken buhn garin da yake dauke da shi.
“Suna cikin bincike sai suka yi arba da harsasan bindigar Ak47 guda 340 da aka boye a cikin garin rogon,” a cewar DSP Edafe.
Ya ce sun tsare Solomon kuma za su shi gaba da gudanar da bincike a kan lamarin gabanin mika shi gaban kotu.