An kama matashi kan luwaɗi da yara 12 a Jigawa
Wani matashi mai shekaru 25 ya faɗa komar ’yan sanda kan zargin zakke wa wasu yara maza 12 a garin Basirka da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a birnin […]
Wani matashi mai shekaru 25 ya faɗa komar ’yan sanda kan zargin zakke wa wasu yara maza 12 a garin Basirka da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram ta Jihar Jigawa.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a birnin Dutse.
- Ƙudirin Dokar Haraji ya tsallake karatun farko a Majalisar Dattawa
- Ƙungiyar Hezbollah ta fara janye mayaƙanta daga kudancin Lebanon
DSP Shiisu ya ce da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin ranar 21 ga watan Nuwamban nan ne aka kama mutum yayin da yake zakke wa wani yaro ta dubura a wani shagonsa da ke ƙauyen Basirka a karamar hukumar ta Gwaram.
Sanarwar ta a ce a yayin bincike ne wanda ake zargi ya yi iƙirarin cewa makamancin wannan laifi ne ya sanya aka kore shi daga garin Zariya na Jihar Kaduna.
DSP Shiisu ya ce cibiyar binciken lafiyar waɗanda aka yi wa fyaɗe ta Jihar Jigawa ta tabbatar da cewa an yi luwaɗi da yaran 12 da ake zargin matashin ya zakke musu.
Kazalika, sanarwar da DSP Shiisu ya fitar ta bayyana cewa rundunar ’yan sandan ta kuma kama wasu mutum bakwai da suka fito daga Karamar Hukumar Gezawa ta Jihar Kano kan zargin satar shanu uku da tumakai 11.
Ya ce za a gurfanar da duk ababen zargin a gaban kuliya da zarar bincike ya kammala.