An kama matashi mai luwadi da yara
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Jihar Ebonyi sun kama wani matashi mai suna Chibuike Maduka sakamakon zarginsa da luwadi da kananan yara a kauyen Ndibe na karamar Hukumar Afikpo ta Arewa.Sai dai a bayanin da ya yi wa jami’an tsaron, wanda ake zargin ya ce mahaifiyarsa Idam Josephine ce ta jefa shi cikin […]
Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Jihar Ebonyi sun kama wani matashi mai suna Chibuike Maduka sakamakon zarginsa da luwadi da kananan yara a kauyen Ndibe na karamar Hukumar Afikpo ta Arewa.
Sai dai a bayanin da ya yi wa jami’an tsaron, wanda ake zargin ya ce mahaifiyarsa Idam Josephine ce ta jefa shi cikin wannan hali da ya tsinci kansa a ciki.
Da take nuna wanda ake zargi ga manema labarai Kwamandar NSDC a shiyyar Abakaliki, Uwargida Ego Echendu, ta ce bayan samun bayanai ne ta sanar da jami’anta su sanya ido sosai kan maganar har sai da aka kama shi, ta ce ya yi ikrarin aikata luwadi da kananan yara.
Uwargida Echendu ta ce “an kyankyasa mana labarin ne na ba jami’aina da ke Afikpo iznin su sanya ido da misalin karfe 3:00 na rana aka same shi ya kwanta da wani yaro har ma ya yi masa rauni a dubura daga nan ne aka cafko shi.”
Kwamandar ta tabbatar da aniyar ofishinta na mika maganar ga ma’aikatar kula da harkokin mata tunda al’amarin ya hada da yara maza domin daukar mataki na gaba.