An kama matashi ya saci giyar N300,000

An gurfanar da wani matashi a gaban kotun kan satar katon 37 na giya da kudinta ya kai Naira 299,000.

An kama matashi ya saci giyar N300,000

KOTU

An gurfanar da wani matashi mai shekara 26 kan satar katon 37 na giya da kudinta ya kai Naira 299,000 a gaban wata kotun majistare da ke zamanta a Jihar Ogun.

’Yan sanda sun gurfanar da shi a gaban kotun ne bisa zargin sa da aikata laifin a ranar 7 ga watan Yunin 2022, a wani kamfani da ke unguwar Igboloye a Ota da ke jihar.

Dan sanda mai gabatar da kara Sufeto E.O Adalarayo ya bayyana wa kotun cewa, wanda ake zargin ya kuma saci batirin mota da kudinsa ya kai Naira dubu 68.

Hakan a cewarsa, laifi ne karkashin sashe na 390 (9) na kundin manyan laifukan 2006 na Jihar Ogun.

To sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifin, inda alkalin kotun ya babda belinsa kan Naira dubu 200 da sharadin kawo masu tsaya masa da ke da wannan kudin.

Alkalin ya kuma ce dole ne masu tsaya masan su kasance suna da takardun shaidar biyan harajin jihar na shekara biyu, sannan ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Yulin da muke ciki.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos