An kama matashin da ya addabi jama’a da sace-sace a Suleja

Wani matashi mai suna Yusuf Yakubu da ake zargi ya jima yana sace-sace a unguwannin garin Suleja da ke Jihar Neja ya shiga hannu, lokacin da ’yan sintiri suka kama shi da wasu kayayyaki da ake zargin ya sato da misalin karfe 2:00 na dare a ranar Alhamis din makon jiya.Yusuf Yakubu da ke zaune […]

An kama matashin da ya addabi jama’a da sace-sace a Suleja

Yusuf Yakubu, dauke da kayan da ake zargi ya sata a garin Suleja.Wani matashi mai suna Yusuf Yakubu da ake zargi ya jima yana sace-sace a unguwannin garin Suleja da ke Jihar Neja ya shiga hannu, lokacin da ’yan sintiri suka kama shi da wasu kayayyaki da ake zargin ya sato da misalin karfe 2:00 na dare a ranar Alhamis din makon jiya.
Yusuf Yakubu da ke zaune a Unguwar Malam Shehu a Suleja, majiyarmu ta ’yan sintirin Unguwar Dauda Gyara suka kama shi lokacin da suka ga yana zirga-zirga cikin dare a yankin, inda suka kama shi dauke da kwamfutar tafi-da-gidanka da kuma wayoyin hannu.
Da suka kai shi ofishinsu a yayin bincike ya sanar da su cewa sato su ya yi, ya kuma sanar da su karin wasu wayoyi da ya sato a lokacin binciken.
Wanda ake zargin ya bayyana musu cewa, ya dauko kwamfutar ce daga wani gida a Unguwar Malam Shehu a wani daki a lokacin da masu kwamfutar suke barci.
Daga bisani ofishin ’yan sintirin ya mika wanda ake zargin ga babban ofishin ’Yan sanda na “A” Dibision, kamar yadda majiyarmu ta tabbatar.   
Yunkurin jin ta bakin babban ofishin ’yan sanda na “A” dibision ya ci tura a lokacin da wakilinmu ya gabatar da kansa ta waya ga kwamandan ’yan sandan Shiyyar Suleja, sai ya bukaci ya sake kiransa, bayan kiran ne kuma, bai dauki wayar ba. Shi kuma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar ASP Richard Adamu ya ce ba ya da masaniya a kan al’amarin.