An kama matashin da ya cinna wa mutane wuta a masallaci a Kano

Matashin mai shekaru 38 ya shiga hannun hukuma bayan da ya cinna wa mutane wuta a lokacin da suke sallar asuba a masallaci

An kama matashin da ya cinna wa mutane wuta a masallaci a Kano

Hedikwatar ‘yan sandan Jihar Kano

’Yan sanda sun kama wani matashi mai shekaru 38 da ake zargin ya cimma wa mutane wuta a lokacin da suke sallar asuba a Jihar Kano.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar cewa binciken farko ya nuna matashin ya yi wannan aika-aika ne a sakamakon rikicin gado.

Aminiya  ta ruwaito cewa an banka wa mutane wuta a lokacin da suke sallar Asuba a wani masallaci da ke kauyen Larabar Abasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa a ranar Laraba.

Shaidu sun ce sai da wanda ake zargin ya shiga masallacin ya rurrufe kofofin ya zuba makamashi ya kyasta wuta sannan ya kulle su a ciki ya tsere.

“Da kyar mutanen da suke waje suka yi nasarar balle kofar su ceto na cikin masallacin,” in ji wani mazaunin yankin.

Wani dattijo da ke salla a masallacin ya ce sai da aka yi raka’a daya an ffara raka’a ta biyu wanda ake zargin ya sa wutar.

Malamin wanda ya ce ba da shi aka fara sallar ba saboda ya makara, ya bayyana yadda mutane suka kokkone a masallacin, kuma akasarin wadanda suka konen dattawan garin ne.

Aminiya ta samu bayani cewa akalla mutane 28 ne suka samu mummunan kuna a sakamakon wutar da mutumin ya cimma a masallacin fa ke garin Larabar Abasawa da ka Karamar Hukumar Gazawa ta jihar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa an kai mutanen da suka kone asibiti domin ba su kulawa a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano.

Majiyoyi a yankin sun ce kimanin mutane 40 ne suke sallar a masallacin a lokacin da mutumin ya yi wannan aika-aika.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano