An kama matashin da ya kashe karuwa yana ciniki da wata
An yi caraf da shi yana tsaka da ciniki da wata karuwar da zai dauka.
Wani matashi mai shekara 18 da ake zargi ya dauki wata karuwa ya kuma kashe ta bayan ya gaza biyan ta kudin lalatar da ya yi da ita ya shiga hannu a lokacin da ya je daukar wata kuma.
Lamarin wanda ya faru a yankin Ilupeju da ke cikin birnin Abeokuta a Jihar Ogun ya dauki hankalin al’ummar yankin.
- Gwamnatin Kaduna ta sake maka El-Zakzaky a kotu
- An kaddamar da mafarauta 1,000 don yaki da Boko Haram a Borno
Kakakin ’yan sanda a Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya ce shugaban al’ummar unguwar Ilupeju ne ya ankarar da ’yan sanda game da lamarin inda ya kai kara a ofishin ’yan sanda da ke Adatan.
Ya shaida masu cewa a ranar 18 ga watan Yuli sun wayi gari da ganin gawar wata mace a yashe a gefen titi kwance cikin jini, an daba mata wuka a wuya aka jefar da wukar a gefen gawar.
Abimbola Oyeyemi ya ce hakan ne ya sanya DPO na yankin, SP Abiodun Salau ya jagoranci wasu ’yan sandan suka baza komarsu na binciken lamarin.
“A binciken da suka yi ne suka gano an yi wa matar mai shekara 28 gani na karshe ne a lokacin tana tare da matashin da ake zargi mai shekara 18, bayan ya dauke ta a wani wuri da karuwai ke yin dandazo da zarar dare yayi a shiyar Pansheke a Abeokuta.
“Hakan ne ya sanyan aka kafa wa masa tarko inda a ranar Alhamis 22 ga watan Yuli, kimanin kwana uku da faruwar lamarin aka yi nasarar kame shi a Pansheka, inda karuwan kan taru, a lokacin da yake tsaka da zance da wata karuwar, yana kokarin daukar ta,” inji shi.
‘Tsohon mainlaifi ne’
Kakakin Rundunar ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa laifin kashe matar, kuma tsohon mai laifi ne da aka sako daga gidan yari kimanin wata daya da ya wuce.
Ya shaida mana cewa ya dauki marigayiyar ne a Pansheke, bayan ya yi lalata da ita ta bukaci ya ba ta kudinta Nnaira dubu goma kamar yadda suka shirya zai biya ta, amma sai ya gaza biya kasancewar dubu takwas ne a hannunsa.
Sai ya ba ta wayar salularsa ya ce ta rike ta jira shi a gefen titi zai je ya ciro kudi, ko da ya dawo sai ya lallaba ya soka mata wuka a wuya, inda ya dauke wayarsa ya bar ta cikin jini.
Tuni dai Kwamishinan ’Yan Sanda Jihar Ogun, Edward Awolowo Ajogun ya ba da umarnin tisa keyar wanda ake zargin zuwa Sashin Binciken Manyan Laifuka na rundunar domin bincike tare da gurfanar da shi a gaban kuliya.