Matashi ya sace ƙodar wani ya sayar a Abuja

An cafke wani matashi da ya yaudari wani dan shekara 17 zuwa Abuja ya cire masa koda ya sayar

Matashi ya sace ƙodar wani ya sayar a Abuja

An cafke wani matashi mai shekaru 20 da ya yaudari wani ɗan shekara 17 zuwa Abuja ya cire masa ƙoda ya sayar.

Wanda ake zargin ya yaudari ɗayan ne daga Jihar Binuwai zuwa Abuja, inda ya hada baki da wasu suka yi masa tiyata, suka sace ƙodarsa suka sayar ba da saninsa ba.

Dan sanda mai gabatar da ƙara, Insfekta Godwin Ato ya shaida wa kotu cewa sauran waɗanda ake zargin sun tsere amma ana ci gaba da farautar su.

Ya bayyana cewa a cikin watan Agusta ne mahaifain wanda aka cire wa ƙodar da ke zaune a Karamar Hukumar Gwer ta Gabas ta Jihar Binuwai, ya kawo ƙara ofishin ’yan sanda cewa a watan Afrilu waɗanda ake zargin suka yaudari dansa suka yi safarar ƙodarsa ba da saninsa ba.

Jami’in ya shaida wa kotun cewa abin da aka yi wa matashin laifi ne karkashin dokar haramta safarar bil Adama, kuma rundunar ’yan sandan jihar na ci gaba da gudanar da bincike a kai.

Bayan sauraron su ne ne alƙalin kotun majisataren, Taribo Atta, ya ba da umarnin tsare wanda ake zargin a babban gidan yari da ke Makurdi, sannan ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Oktoba.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna