An kama matashin da ya yi kutse a coci cikin shigar mata
Wani matashi mai matsakaicin shekaru da ba a bayyana sunansa ba, ya shiga hannun ’yan Sanda a Jihar Gombe a lokacin da ya yi shigar mata ya nufi wani cocin ECWA a garin billiri da ke Jihar. Matashin wanda ya yi kitso a kansa irin na mata kuma ya yi shiga irin ta mata a […]
Wani matashi mai matsakaicin shekaru da ba a bayyana sunansa ba, ya shiga hannun ’yan Sanda a Jihar Gombe a lokacin da ya yi shigar mata ya nufi wani cocin ECWA a garin billiri da ke Jihar.
Matashin wanda ya yi kitso a kansa irin na mata kuma ya yi shiga irin ta mata a ranar Kirsimeti a karamar Hukumar billiri, ya doshi cocin da nufin zai shiga, kuma binciken da ake yi wa mutane kafin a shiga ne ya sa aka gane cewa ba mace ba ce, namiji ne.
Bayan da aka kama shi, an yi tsammanin dan Boko Haram ne ya bad da kama don ya shiga cocin ya tada bam, amma sai aka ga babu komai a jikinsa, shigar ce kawai ya yi irin ta mata. Koda da ya ji matsi sai ya ce shi ba dan Boko Haram ba ne, shi dan daudu ne.
A lokacin da wakilinmu ya tuntubi Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Gombe, DSP Fwaje Attajiri, ya tabbatar da faruwar hakan, sannan ya ce jami’ansu ne na farin kaya suka kama matashin a cocin na ECWA da ke garin billiri amma ba a same shi da wani abin fashewa ba kamar yadda wasu ke ta yayatawa a kafar sadarwa ta Facebook.
Ya ce suna nan suna gudanar da bincike a kansa don jin mene ne ya sa shi yin wannan shiga ta mata kuma ya nemi shiga wajen ibada a lokacin bikin Kirsimeti kuma da zarar sun kammala bincikensu za su tura shi zuwa kotu.
A wani labari mai alaka da wannan, Sarkin billiri Dokta Abdu Buba Mai Sherru na II, a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa a garin billiri kan yadda aka gudanar da bikin Kirsimeti a masarautarsa; ya ce ba su samu wani tashin hankali ba sai dai rahoton wannan saurayi da ya yi shiga ta mata, ya yi yunkurin shiga coci, wanda ba su san da wacce irin manufa ya zo ba.
Sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta kara inganta tsaro a ko’ina a fadin jihar sannan kuma a taimaki DPO na yankin da motar aiki, domin ba ya da motar aiki kuma yana da kokarin yin aikin.
Daga nan sai ya yi amfani da wannan dama wajen aike wa da daukacin jama’ar karamar Hukumar biliiri da Jihar Gombe da Najeriya baki daya sakon fatan alheri na bikin Maulidi da Kirsimeti da sabuwar shekara.