An kama matashin da ya yi wa ’yar shekara 5 fyade a Gombe
Rundunar ta ce za ta mika shi kotu da zarar ta kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mai shekara 20 da ake zargi da yi wa wata yarinya ’yar shekara biyar fyade.
Da yake gabatar da wanda ake zargin, kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce wanda ake zargin wanda mazaunin unguwar Tike ne a garin Bajoga a Karamar Hukumar Funakaye ya shiga hannu.
- Wa zai fi samun kudi: Tsakanin Messi a Inter Miami da Ronaldo a Al-Nassr
- Buhari ya kashe wa matattun matatu fiye da kudin gina Matatar Dangote —Gwamnan Nasarawa
Ya ce wani mai suna Yahaya Isah, ne ya kai rahoton faruwar lamarin ofishin ’yan sanda na garin Bajoga, inda ya ce suna zargin matashin da zakkewa yarinyar ta dubura a bayan wata makarantar almajirai da ke garin na Bajoga.
A cewar kakakin rundunar, suna karbar rahoton suka je suka kamo matashin a gidan mahaifiyarsa, wanda daga bisani ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.
Ya ce an kai yarinyar asibiti domin duba lafiyarta, kuma ya ce da zarar sun kammala binciken za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.
Sai dai wanda ake zargin ya roki hukuma da ta yi masa sassauci kan laifin da ake zargin ya aikata.