An kama ‘matsafiya’ da kayan ’yan makaranta

Matar ta ce wani mai Jeep na yin lalata da ita ya ba ta ruwan roba.

An kama ‘matsafiya’ da kayan ’yan makaranta

‘Yan sanda

Wata mata da ake zargi matsafiya ce da ke yin shigar burtu kamar mahaukaciya a gefen wani titi ta shiga hannun jama’ar gari.

Dubun matar ta cika ne bayan mazauna sun hango ta da tsakar dare tana sanya wasu kaya da ake zargin sassan jikin dan Adam ne a cikin wata motar kirar Jeep a kusa da inda take zama a unguwar Zango da ke Ilori a Jihar Kwara.

Ganin haka, ’yan banga da ke yakin Kulende inda matar ta shafe shekaru tana zaune suka yi kokarin gano abin da matar ke yi da mai motar, amma suna zuwa kusa da wurin, sai Jeep din ta fita a sukwane.

Hakan ya sanya shakku a zukataun mutanen yakin Kulende da ke Zango, inda matar ta shafe shekaru tana zaune, suka cafke ta a ranar Alhamis din da dare.

Wani mazaunin unguwar, Mista Kudus ya shaida wa wakilinmu cewa bayan nan ne ’yan banga suka fara bincikar kayan matar, inda suka gano tulin takardun kudi da ruwan roba da wata wuka da kuma fiya daya na kayan makarantar kananan yara da litattafai da jaka da taklmin makaranta.

Mista Kudus ya ce hakan ne ya sa aka titsiye ta domin yi mata tambayoyi, amma ta kasa yin bayanin yadda ta samo kayan makarantar.

Ya ce daga nan aka wuce da ita, yanzu tana tsare a Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) da ke Hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara a garin na Ilori.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwa lamarin, inda ya ce suna kokarin kamo mai motar.

Ya bayyana cewa kkudadin da aka gani a wurin matar Naira dubu 166,700.

A cewarsa, “Matar ta bayyana mana cewa mutumin da ke cikin Jeep din ya je ne domin  yin lalata da ita, sannan ya ba ta ruwa.

“Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kwara, Tuesday Assayamo, ya bayar da umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin gami da kai matar zuwa asibiti domin tabbatar da yanayin hankalinta,” inji shi.

Zaɓen Edo: Yadda aka kama masu sayen ƙuri’a da ’yan daba

Sarakunan Nijar sun kai wa Gwamnatin Yobe ziyarar jaje

Ɗan majalisa ya yi jinjina kan naɗa Danyaya Sarkin Ningi

’Yan Sanda sun kama gungun ’yan fashi 7 a Katsina