An kama miji da mata kan satar buhunan shinkafa a gidan marayu

Mijin wanda yake sana’ar gadi ya alaƙanta abin da suka aikata da sharrin Sheɗan.

An kama miji da mata kan satar buhunan shinkafa a gidan marayu

Amotekun

Wani miji da mata sun shiga hannu kan zargin satar buhunan shinkafa da kayayyakin abinci a wani gidan marayu da ke Jihar Ondo.

Askarawan tsaro mallakar Jihar Ondo waɗanda aka fi sani da jami’an Amotekun ne suka cafke ma’aurantan bayan tattara bayanan sirri kan ta’asar da suka aikata.

Bayanai sun ce ababen zargin—John Avor mai shekaru 42 da matarsa, Mary Avor mai shekaru 38—sun shiga gidan marayun ne da ke Unguwar Shagari a Akure, babban birnin Ondo.

Yayin da ake yi wa manema holen ababen zargin, Kwamandan Amotekun, Adetunji Adeleye, ya ce ma’aurantan tare da wasu ’ya’yansu masu ƙananan shekaru sun buɗe gidan marayun cikin duhun dare inda suka yi awon gaba da buhunan shinkafa.

Adeleye ya ce ana zargin iyalan sun kuma wawushe duk buhunan shinkafa a wani shago da ke makwabta da gidan marayun.

A cewarsa, iyalan sun yi ƙaurin suna wajen shiga gidaje da shaguna suna satar kayayyakin abinci da suke kai wa wani da ya saba sayen kayayyakin.

“Mun kama waɗannan iyalan ne da suka haɗa da miji da matarsa da kuma ’ya’yansu biyu da suka saba shiga gidajen jama’a suna satar kayayyakin abinci. A taƙaice dai waɗannan iyalan barayi ne.

“Akwai ’ya’yansu guda biyu masu shekaru 12 da 15 da muka kama tare da sh, sai dai saboda wasu dalilai ba za mu iya yi wa manema labarai holensu ba saboda ƙarancin shekarunsu.”

Da yake yi wa manema labarai jawabi, magidancin mai suna Avor wanda ya ce yana sana’a ta aikin gadi, ya alaƙanta abin da suke aikatawa da sharrin Sheɗan.

Kazalika, jami’an na Amotekun sun yi manema labarai holen ƙarin wasu ababen zargi 20 da suka aikata laifuka daban-daban a jihar.

A ƙoƙarin da take yi  na karkaɗe miyagu a jihar, Kwamandan Amotekun ya ce jami’ansa da ke sashen bincike da tattara bayanan sirri na musamman sun cafke wasu ƙasurguman masu garkuwa da mutane biyar yayin da suka shiga sintiri dajin Elegbeka.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja