An kama mijin malama yana mata satar jarabawa
Jami’an tsaro sun cafke mijin wata malama da ya batar da kama domin yi mata satar jarabawar neman aikin koyarwa a makarantar gwamnati. Dubun magidancin ta cika ne bayan bambancin da aka gano a hotonsa da na matar tasa wadda bayananta da hotonta ne ke kan takardun neman aikin da ke Ma’aikatar Ilimi. Ba’amurkiyar da […]
Jami’an tsaro sun cafke mijin wata malama da ya batar da kama domin yi mata satar jarabawar neman aikin koyarwa a makarantar gwamnati.
Dubun magidancin ta cika ne bayan bambancin da aka gano a hotonsa da na matar tasa wadda bayananta da hotonta ne ke kan takardun neman aikin da ke Ma’aikatar Ilimi.
- Ba’amurkiyar da ta kashe dan Najeriya ta shiga hannu
- Rarara: Ina wakar Buhari da ’yan Najeriya suka biya kudade?
- ’Yan sanda sun yi wa ’yan bindiga luguden wuta a Zamfara
- Mayakan Boko Haram sun kai hari Geidam
An kama shi ne a wata cibiyar rubuta jarabwar daukar malamai da ke Kwalejin Ilimi da ke Ilesha a Jihar Osun, inda aka mika shi ga jami’an hukumar tsaro ta NSCDC.
Jami’ar Yada Labaran Ma’aikatar Ilimin Jihar, Roseline Olawumi, da abin ya faru a kan idonta ta tabbatar da cewa mutumin ya je cibiyar ce da nufin yi wa matar tasa jarabawar.
Kwamishinan Ilimin Jihar, Folorunsho Oladoyin ya yi tir da abin, yana mai cewa babban abin kunya ne a samu mai mai son zama malami ya dauko sojan haya ya yi masa magudin jarabawa.
“Abin kunya ne a samu wanda zai koyar da dalibai ilimi da tarbiya yana aikata magudi, to wani irin abin koyi zai zame wa daliban? Wannan babban abin takaici ne.
“Ina amfani da wannan dama wurin kira ga matasa da su gaskiya da mutucin shi ne kadai hanyar samun nasara,” inji shi.