An kama mutanen da ‘suka ci balangun gawar ‘Yan sanda’
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta damke mutanen da ake zargin sun yanki naman gawar ‘yan sanda suka cinye a lokacin zanga-zangar #EndSARS. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na jihar, SP Olugbenga Fadeyi, ya fada wa Aminiya a yanzu haka an kai su Hedikwatar ‘Yan sanda da ke Abuja don ci […]
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta damke mutanen da ake zargin sun yanki naman gawar ‘yan sanda suka cinye a lokacin zanga-zangar #EndSARS.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na jihar, SP Olugbenga Fadeyi, ya fada wa Aminiya a yanzu haka an kai su Hedikwatar ‘Yan sanda da ke Abuja don ci gaba da gudanar da bincike.
- An kama mai abincin sayarwa da ke girki da ruwan wanke gawa
- ’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda sun sace makamai
Daga cikin wadanda aka kama, an ce wata mata ‘yar shekara 34 ta yanki tsokar gawar dan sanda ta cinye.
Sai dai kuma ta ki amincewa da zargin a lokacin da ake gudanar da bincike, amma ta ce wani mutum dan shekara 43 ya ba ta gasasshen naman domin ta ajiye masa.
Da ya ke kare kansa, abokin laifin nata ya amince yana wajen da aka kashe ‘yan sanda tare da wasu ‘yan daba, amma matar ta yanki gawar ta roke shi ya ba ta hankici ko tawul ta kunshe naman a ciki.
Jami’an sun hadu da ajalinsu ne bayan an kai su birnin Badun aikin kwantar da tarzomar #EndSARS a ranar 22 ga watan Oktoba.