An kama mutanen da suka kashe mutumin da suke zargin lalata da mahaifiyarsu
’Ya’yan sun cika umarnin mahaifin nasu inda suka kashe kuma suka kone gawar mutumin.
Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta tabbatar da cafke wani basarake da ’ya’yansa biyu bisa kashe wani mutumin kauyen Dako Kangarwa da ke Karamar Hukumar Yunusari kan zargin neman matar basaraken.
Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Damaturu.
- Zan so na koyi yadda Ahmed Lawan zai koma majalisa ba tare da takara ba — Okorocha
- Dalilin da aka kai samame gidan Matawalle — Gwamnatin Zamfara
Ya ce ababen zargin sun aikata laifin ne a ranar 7 ga watan Yuni bayan mutanen uku sun zargi mutumin da yin lalata da matar basaraken kuma mahaifiyar yaran biyu.
Kamar yadda wata majiya kuma ganau ta bayyana, wadanda aka cafke sun yi wa mamacin yankan rago ne, sannan suka kone gawarsa kurmus.
“Kamar yadda aka ruwaito, lamarin ya fara ne da fada da ya kai ga mamacin ya yi amfani da wuka wajen raunata mahaifin wadanda ake zargin da kisan gillar,” in ji Abdulkarim.
Ya kara da cewa daga baya basaraken ya umurci ’ya’yansa da su nemo duk inda ya shiga har sai sun ga bayansa.
Wakilinmu ya ruwaito cewa hakan ce ta sanya nan take suka cika umarnin mahaifin nasu, inda suka bi shuka kashe shi sannan suka kone gawarsa.
Kakakin ’yan sandan ya ce mutanen uku sun mika kansu ga ofishin ’yan sanda na Yunusari bayan faruwar lamarin.
Sai dai ya ce sun mika kan nasu ne a yayin da dara ta ci gida a kokarinsu ne nema wa basaraken magani a sakamakon raunin da ya ji.
“Daga baya, wadanda suka aikata wannan danyen aikin sun kai rahoton kansu ga rundunar a Yunusari bayan jin labarin kama mahaifinsu,” in ji shi.
Abdulkarim ya ce an mika mutanen uku zuwa sashen binciken manyan laifuka domin ci gaba da bincike.
Kakakin ya ce an ajiye gawar mutumin a Asibitin kwararru da ke Damaturu domin gudanar da binciken kwakwaf kafin a mika gawarsa ga iyalensa.