An kama mutum 2 sun yi wa wata mata fashi a Abuja

Rundunar ta ce za ta gurfanar da su a kotu da zarar ta kammala bincike.

An kama mutum 2 sun yi wa wata mata fashi a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta kama wasu da ake zargi ’yan fashin “one chance” ne bayan sun yi wa wata mata fashi a kan titin Giri zuwa Lugbe da ke kan hanyar zuwa titin jirgin saman Abuja.

Kwamishinan ’yan sandan Abuja, Ahmed Mohammed Sanusi, ya ce jami’an rundunar da ke sintiri domin yaƙi da laifuka ne suka kama mutanen.

Ya bayyana cewa jami’an sun tarar da wata matashiya tana kuka tana neman taimako.

Bayan sun tambaye ta abin da ya faru, ta shaida musu cewa wasu ’yan “one chance” sun ƙwace mata kayanta sannan suka jefar da ita a hanya.

Nan take jami’an suka fara bincike tare da tare wata mota ƙirar Volkswagen Golf mai lamba SKK 567 AG, inda suka kama mutane biyu; Muhammed Muhammed mai shekara 22 da Muhammed Saidu mai shekara 20.

A yayin binciken motar, jami’an sun gano kayan matar da aka sace, ciki har da kwamfuta, waya ƙirar iPhone da kuma cajar waya.

Haka kuma, an samu wuƙa guda biyu da almakashi guda ɗaya a cikin motar.

Kwamishinan ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka tare da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Sannan ya buƙaci mazauna Abuja su riƙa kai rahoton duk wani mutum ko wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa da su.