An kama mutum 3 sun yi wa ’yar shekara 12 fyade a Bauchi

Wasu mutum hudu sun shiga hannu kan  aikata fyade, ciki har da wasu uku da ake zargi sun yi wa wata karamar yarinya fyade a garin Jalam da ke Karamar Hukumar Dambam a Jihar Bauchi.

An kama mutum 3 sun yi wa ’yar shekara 12 fyade a Bauchi

Wasu mutum uku da ake zargi da aikata laifi (Daga taskarmu).

Mutum hudu sun shiga hannu kan  aikata fyade, ciki har da wasu uku da ake zargi sun yi wa wata karamar yarinya fyade a garin Jalam da ke Karamar Hukumar Dambam a Jihar Bauchi.

Rundunar ’yan sandan jihar ta kama wani matashi dan shekara 27 bisa zargin lalata da wata ’yar shekara bakwai a Karamar Hukumar Itas Gadau ta jihar.

Masu fyaden da ka kama a Jalam, sun yaudari yarinyar ne lokacin data ke tallar awara a wajen Kasuwar Dambam kafin daga bisani suka yi mata fyade daya bayan daya.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa ’yan jarida cewa lamarin ya faru ne a lokacin da wani likitan da ke aiki a babban asibitin Dambam ya sanar da yan sanda.

Ya ce, “Da misalin karfe 11:30 na safe, iyayen wata yarinya ’yar shekara 12 suka kawota asibiti domin a duba lafiyarta.

“Da samun labarin, jami’an tsaro karkashin jagorancin Baturen ’Yan Sanda (DPO) na Dambam sun ziyarci asibitin kuma suka kaddamar da bincike na gaskiya kan lamarin.”

Wakil ya ce bincike ya kai ga kama wasu mutum uku kuma, “Lokacin da ake yi musu tambayoyi, duk wadanda ake zargin sun amsa laifinsu.

“Ana ci gaba da gudanar da bincike, daga nan ne za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Rufe ‘boda’ ya kawo yunwa da rashin aiki a Arewa —CNG

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024