An kama mutum 33 da ake zargi da hannu a harin cocin Kwara
Yayin samamen, waɗanda ake zargin sun jefar da makamin harbo jirgin sama da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku, waɗanda daga bisani ’yan sanda suka ƙwato
‘Yan sanda
’Yan sanda sun kwato makamin harbo jirgin sama da wasu muggan makamai a hannun mutanen da ake zargi da yin garkuwa da mutane a coci a Jihar Kwara.
Rundunar ’Yan Sanda ta Najeriya ta bayyana hakan ne a yayin da take sanar ta kama aƙalla mutum 33 da ake zargi mambobin wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ke da alaƙa da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami.
A ranar Litinin rundunar ta sanar a ranar cewa jami’anta na sashen tattara bayanan sirri sun kuma ƙwato makamin harbo jirgin sama da wasu manyan makamai.
Mai magana da yawun rundunar, Anthony Placid, ne ya shaida wa taron manema labarai a Abuja cewa, an kama waɗannan mutane 33 ne a wasu hare-hare da aka tsara tare a jihohin Kwara da Kogi, bayan binciken da aka gudanar kan harin da aka kai wa cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku a Jihar Kwara a watan Nuwambar 2025.
Aminiya ta rawaito cewa, a lokacin harin, ’yan bindiga sun kashe aƙalla masu ibada uku tare da sace mutum 38 a cocin, ciki har da fasto, yayin da ake gudanar da ibada.
- Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami
- 2027: ’Yan ADC a Majalisar Wakilai sun buƙaci a binciki shugaban INEC
An kuma nuna harin kai tsaye a kafafen sada zumunta, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma a fadin ƙasa, kafin daga bisani a ceto waɗanda aka sace bayan wani haɗin gwiwar jami’an tsaro.
Da yake ba da karin bayani, Placid ya ce binciken farko ya nuna cewa waɗanda ake zargin na da hannu a haɗa baki wajen aikata laifuka, fashi da makami da kuma garkuwa da mutane.
Sauran laifukan da ake danganta su da su sun haɗa da satar shanu, kisan kai, mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, safarar makamai da kuma ayyukan ta’addanci.
Ya ƙara da cewa kayan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda bakwai, zungurun alburusai guda bakwai, makamin harbo jirgin sama guda ɗaya, harsasai masu rai 32 na 7.62mm, na’urorin sadarwa na walkie-talkie guda biyar da kuma jakar baya mai launin sojoji.
Placid ya ce, “Bayan harin da aka kai wa cocin C.A.C a garin Eruku, Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, jami’an IRT, bisa sahihan bayanan sirri na mutane da fasaha, sun gudanar da hare-hare a jihohin Kwara da Kogi.
“Binciken farko ya nuna cewa ƙungiyar na da hannu a haɗa baki wajen aikata laifuka, fashi da makami, satar mutane, satar shanu, kisan kai, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, safarar makamai da kuma ayyukan ta’addanci, wanda aka riga aka samu hujjoji a kansu.
“An kama mambobin ƙungiyar a wurare daban-daban da suka haɗa da Gbugbu, Ora-Ago, Baballa, Kaiama, Awi, Charagi, Patigi da Okeode.
“Yayin samamen, waɗanda ake zargin sun jefar da makamin harbo jirgin sama da bindigogi ƙirar AK-47 guda uku, waɗanda daga bisani ’yan sanda suka ƙwato. Ana ci gaba da bincike domin cafke sauran mambobin da suka tsere da kuma ƙwato ƙarin makamai.”