An kama mutum 4 da albarusai dubu 10 da suke sayarwa ‘yan fashi a Ibadan
Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama mutum 4 da albarusai dubu 10 da suka boye a cikin wani gida a Unguwar Oke-Bola a Ibadan inda zargin suna sayarwa ga ’yan fashi da makami. Da yake nuna mutanen tare da baje kolin albarusan da wasu motoci 2 mallakar wadanda aka kama ga taron ’yan jarida, […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Oyo ta kama mutum 4 da albarusai dubu 10 da suka boye a cikin wani gida a Unguwar Oke-Bola a Ibadan inda zargin suna sayarwa ga ’yan fashi da makami. Da yake nuna mutanen tare da baje kolin albarusan da wasu motoci 2 mallakar wadanda aka kama ga taron ’yan jarida, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu, ya nuna jin dadi kan yadda suka samu labarin sirri daga mutane da ya kai ga bankado maboyar makaman.
Mutanen da aka kama masu suna Adekunle Abimbola da Abel Kojo da Mukaila Ariyo da Ade Adebayo ana zargin sun dade suna dillancin albarusai ga ’yan fashi da makami da sauran miyagun da suka addabi jama’a a ciki da wajen birnin Ibadan, kamar yadda Kwamishinan ya sanar.
Kwamishinan ’Yan sandan ya kuma nuna wadansu ’yan mata biyu masu suna Ajoke Abu da Azeezat Isma’ila da aka kama su dauke da bindiga da albarusai inda suka ce, suna yi wa samarinsu ’yan fashi da makami aikin jigilar bindigogin ne daga Legas zuwa Iseyin a Jihar Oyo inda suke gudanar da danyen aikinsu.
Ya ce, bincike ya nuna cewa, samarin suna amfani da ’yan matan ne wajen boye makaman domin tsallake shingen binciken jami’an tsaro a kan hanya.
Har ila yau Kwamishinan ya nuna wadansu mutum 10 da ya ce, ’yan damfara ne da suke amfani da sunan bankin bayar da rance ga kananan ’yan kasuwa na bogi a garin Lakwaja a Jihar Kogi. Mutanen sun guje wa kamen jami’an tsaro a Jihar Kogi ne suka sauka a otel din S.L da ke Unguwar Boluwaji a birnin Ibadan inda suka fara damfarar mutane ta amfani da takardun bankin Micro Finance mai suna STAAGMART da ke Oyingbo a Legas suna cutar mutane.
A tare da mutanen da aka kama an samu jimillar Naira dubu 961 da 375 da takardu masu dauke da hatimin Kamfanin Staagmart da wasu layu da guraye.
Kwamishinan ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da dukkan mutanen da aka kama a kotu domin yanke musu hukunci.
Kwamishina Shina Olukolu, ya yi kira ga mazauna Jihar Oyo su rika taka-tsantsan wajen hawan babur na ’yan Okada mai dauke da goyon mutum 1 ko 2 musamman a lokutan asubahi da cikin dare domin a wadannan lokuta ne ’yan Okadan suke yi wa fasinjojinsu fashi da makami da satar mutane domin garkuwa da su.