An kama mutum 4 da kasusuwan dan Adam a Gombe
Za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.
’Yan sanda sun cafke wasu mutum hudu dauke da kasusuwan jikin dan Adam a Jihar Gombe.
Kakakin ’yan sandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ya shaida wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa an kama mutanen ne bayan korafe-korafen da wasu mazauna Jihar Taraba suka yi a kansu.
- ’Yan ta’addan ISWAP 82 sun nitse a ruwa suna kokarin tsere wa sojoji
- ’Yan kwadago sun bukaci Tinubu ya mayar da mafi karancin albashi N200,000
ASP Mahid Abubakar, “Wani Isa Musa daga Karamar Hukumar Bali ta Jihar Taraba ya zo Jihar Gombe don ganawa da wani Alhaji Auwal, inda ya shaida wa daya daga cikin abokan Alhajin cewa zai yi musu addu’ar samun daukaka a kasuwancinsu.
“Auwal ya karbi kudi Naira 650,000 daga hannunsu, amma bayan wani lokaci da masu korafin suka ga babu wani ci gaba a kasuwancinsu, sai suka bukaci ya dawo musu da kudinsu,” in ji shi.
Ya ce daga baya ne Auwal ya mika su ga wani mutum mai suna Ibrahim Adamu mai shekara 65 a Karamar Hukumar Dukku a Jihar Gombe kuma tun a wancan lokacin Auwal ya gudu.
Kakakin ya ce a yayin binciken, wani Ibrahim Adamu na yankin Bagadaza a Gombe ya shiga hannu, inda aka kama shi a gidan Auwal tare da wasu layu da kasusuwan mutane kasar kabari, da sauran kayayyakin tsafi.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da kokarin cafke babban wanda ake zargi, wato Auwal, sauran da aka kama kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.