An kama mutum 400 da ake zargi da kona motar ‘Yan sanda a Abuja
A yayin arangamar mabiya kungiyar shi’a da jami’an tsaro da aka sake yi a Abuja jiya Talata ‘yan shi’an sun kona motar ‘yan sanda. ‘Yan shi’an dai sun watsu a wasu yankunan cikin birnin Abuja wadanda suka hada unguwannin Maitama da Asokoro da Wuse 2. Mabiyan Shi’an na gangamin cewa, gwamnati ta saki shugaban su […]
A yayin arangamar mabiya kungiyar shi’a da jami’an tsaro da aka sake yi a Abuja jiya Talata ‘yan shi’an sun kona motar ‘yan sanda.
‘Yan shi’an dai sun watsu a wasu yankunan cikin birnin Abuja wadanda suka hada unguwannin Maitama da Asokoro da Wuse 2. Mabiyan Shi’an na gangamin cewa, gwamnati ta saki shugaban su Sheikh Ibrahim Zakzaky.
‘Yan kungiyar dai sun ta jifan jami’an ‘yan sandan da duwatsu da dai sauran wasu abubuwa da nufin janyo rikici. Hukumar ‘yan sandan sun ce, sun kama mutum 400 da ake zarginsu da afkawa ‘yan sandan.