An kama mutum 5 kan zargin satar wayar wutar lantarki a Katsina
Rundunar ta ce za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar wayar wutar lantarki da sauran kadarorin gwamnati a ƙauyen Bugaje da ke Ƙaramar Hukumar Jibia.
’Yan sanda sun ce kamen ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu a ranar 9 ga watan Yuni kan mallaka da sayar da kadarorin jama’a ba bisa ƙa’ida ba.
- APC: Inuwa ya gabatar da ɗan takarar gwamnan Gombe ga Tinubu
- Bello Turji ya ɗauki alhakin kashe sojoji a Sakkwato
Daga cikin waɗanda aka kama akwai Hassan Ibrahim mai shekaru 30, Lawal Ibrahim mai shekaru 31.
Sauran sun haɗa da Abubakar Sani mai shekaru 31, kuma an kai su Hedikwatar ’Yan Sanda ta Jihar domin ci gaba da bincike.
Bincike ya nuna cewa wayar wutar lantarki da suka faɗi sakamakon mummunan yanayi kusan watanni shida da suka gabata an adana su ne ƙarƙashin kulawar shugabannin al’umma domin jiran matakin gwamnati.
Sai dai ana zargin waɗanda aka kama da cire wasu daga cikin wayoyin tare da sayar da su ba tare da izini ba.
’Yan sanda sun ce Umar Isa mai shekaru 35 ne ya sayar wa Ibrahim Rabiu mai shekaru 27 da kayan.
Waɗanda ake zargin sun amsa cewa sun sayar da kayan har sau biyar, inda suka samu kuɗi Naira 300,000.
A yayin samamen, jami’an tsaro sun ƙwato ƙofofin ƙarfe guda 10 da ake zargin an sato su daga rukunin gidaje na Barawa, tare da wayar wutar lantarki.
Haka kuma, waɗanda ake zargin sun bayyana sunayen wasu mutum bakwai da ake zargin suna da hannu a lamarin, waɗanda har yanzu ba a kama su ba.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Katsina, Ali Umar Fage, ya yi gargaɗi kan lalata da satar kadarorin gwamnati.
Ya ce irin waɗannan laifuka na hana ci gaba da kuma barazana ga tsaron al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su riƙa kai rahoton duk wani abu da suke zargi ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
Ya ce za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.