An kama mutum 6 bisa zargin kashe basarake
Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ta bayar da karin haske dangane da cafke wasu da ake zargi da hada baki suka sace basaraken gargajiya na Ubulu-Uku, Edward Akaeze Ofulue na 3. Inda ta ce ya zuwa yanzu ta yi nasarar cafke mutum shida daga cikinsu, a jihohi daban-daban na kasar nan, da suka hada da […]
Rundunar ’yan sandan Jihar Delta ta bayar da karin haske dangane da cafke wasu da ake zargi da hada baki suka sace basaraken gargajiya na Ubulu-Uku, Edward Akaeze Ofulue na 3. Inda ta ce ya zuwa yanzu ta yi nasarar cafke mutum shida daga cikinsu, a jihohi daban-daban na kasar nan, da suka hada da Adamawa da Delta da kuma Sakkwato.
Da yake gabatar wa manema labarai mutanen a ranar Talatar da ta gabata, Kwamishinan ’yan sandan Jihar Delta, Alkali Baba Usman ya ce: “Tashin farko, asirinsu ya tonu ne ta hanyar wayar basaraken, kirar Samsung da aka gano a hannun Jamilu Ahmed, bayan samun nasarar kama shi a kasuwar Abraka. Kuma yayin da muka damke shi, ya yi mana bayanin da muka gamsu da shi, wanda ta sanadin haka ne muka yi katarin kama Umar Abubakar. Shi kuma a bayaninsa, ya ce wani mai suna Money-Dey ne ya ba shi dillancin wayar.”
Ya ci gaba da cewa, sauran kuma jagoransu mai suna Usman Musbau, da aka kama kwanaki hudu da faruwar lamarin, ya goge dukkanin wasu muhimman bayanai da ke cikin wayar basaraken kafin ya sayar da ita. Shi kuma Suleiman Musa, ya amsa laifinsa bayan da aka tuhume shi. Ya ma fada wa ’yan sandan cewa akwai wata mace cikinsu mai suna Farida, ita kuma a Jihar Adamawa aka kamo ta, ta hanyar wayar hannu ta fadar basaraken.
Kwamishinan ya ce, shi kuwa Garba Abubakar da ake wa lakabi da Dogo, an kamo shi ne a wata rugar Fulani mai suna Alfarma da ke karamar Hukumar Tangaza, Jihar Sakkwato kuma ya furta cewa shi ya san ya karbi Dala1,100 daga hannun basaraken. Ya ce rundunarsa ta dukufa farautar sauran wadanda suka tsere kuma da zarar sun shiga hannu, kotu za su mika su bayan gama bincikensu. Yanzu haka dai ana ci gaba da binciken sauran da suka shigo hannu.