An kama mutum 6 da ake zargin ’yan Boko Haram ne a Kamaru

Hukumoni a Kamaru sun tabbatar da kama wasu mutum shida da ake kyautata zaton cewa suna da hannu wajen garkuwa da wasu ‘yan kasar China 10, wanda aka yi garkuwa da su a garin Waza da yake lardin Arewa mai Nisa na kasar. Fiye da kwana 30 kenan da aka sace ’yan Chinan kuma har […]

An kama mutum 6 da ake zargin ’yan Boko Haram ne a Kamaru
An kama mutum 6 da ake zargin ’yan Boko Haram ne a Kamaru

Hukumoni a Kamaru sun tabbatar da kama wasu mutum shida da ake kyautata zaton cewa suna da hannu wajen garkuwa da wasu ‘yan kasar China 10, wanda aka yi garkuwa da su a garin Waza da yake lardin Arewa mai Nisa na kasar.
Fiye da kwana 30 kenan da aka sace ’yan Chinan kuma har yanzu suna ci gaba da kasancewa a hannun mutanen da suke garkuwa da su. Kuma har kawo yanzu ba a kai ga gano inda suke ba.
Jami’an tsaro sun bayyana  cewa uku daga cikin wadanda aka kama ’yan asalin Najeriya ne, amma ba su yi bayanin  inda sauran ukun suka fito ba.
Ko da yake har zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki  alhalin sace mutanen, amma hukumomi a Kamaru suna ambatar sunan kungiyar Boko Haram kuma an bayyana cewa mutanen da suka shiga hannu na da nasaba da ita.