An kama mutum 6 kan zargin kisan matafiya 2 a Kaduna
Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya ce ɗaukar doka a hannu babban laifi ne.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta kama mutum shida da ake zargi da kashe wasu matafiya biyu bayan an zarge su da yin sata a ƙauyen Gidan Kalu, da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Yero.
Lamarin ya faru ne a ranar 1 ga watan Yuli, 2026, lokacin da Muhammadu Sani, mai shekara 45, da abokinsa Aliyu Mohammed, mai shekara 40, suke kan hanya zuwa Tudun Wada da ke Zariya domin ziyartar wani kawunsu da ke jinya.
- An tsare Kurfi kan zargin gwamnatin Katsina da ɗaukar nauyin ’yan bindiga zuwa Hajji
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Sakkwato
’Yan sanda sun ce yayin da mutanen biyu ke wucewa ta Gidan Kalu a kan sabon babur, wasu mazauna ƙauyen sun fara zargin su da cewa ’yan fashi ne, inda suka fara ihun “ɓarayi”.
Saboda tsoro, mutanen biyu suka gudu suka bar babur ɗin, amma wasu fusatattun mutane suka bi su tare da kai musu hari.
Rundunar ’yan sandan ta ce an yi musu dukan da ya yi ajalinsu.
Bincike ya nuna cewar wasu daga cikin waɗanda suka ka yi ajalinsu sun san mutanen biyun amma ba su hana abin da ya faru ba.
Bayan samun rahoton lamarin, jami’an ’yan sanda daga Ofishin ’Yan Sandan Birnin Yero sun isa wajen tare da kama Abdullahi Mukailu Kigo da wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a kisan.
’Yan sanda sun ce waɗanda ake zargin sun amsa cewar suna da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da bincike domin gano sauran waɗanda ke da hannu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Kaduna, Rabiu Muhammad, ya yi Allah-wadai da lamarin, inda ya bayyana cewa ɗaukar doka a hannu babban laifi ne.
Ya ce duk wanda aka samu da hannu a kisan zai fuskanci hukunci a gaban kotu.
Ya kuma yi kira ga jama’a su guji ɗaukar doka a hannu, su riƙa kai rahoto ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike.