An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

“Taƙaitacciyar ƙididdigar laifuffukan da aka yi a shekarar 2024 ta nuna cewa an samu ƙararraki 794; An kama mutane 859 da ake zargi da aikata laifuka;

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda

Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da kama wasu mutane 859 a Jihar Filato bisa laifuka daban-daban da suka haɗa da fashi da makami da garkuwa da mutane a cikin shekarar 2024.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin da yake yi wa manema labarai ƙarin haske game da sake kama wasu mutane 27 da aka gabatar da su a hedikwatar rundunar da ke Jos, babban birnin jihar.

Kwamishinan ya ce, “Taƙaitacciyar ƙididdigar laifuffukan da aka yi a shekarar 2024 ta nuna cewa an samu ƙararraki 794; An kama mutane 859 da ake zargi da aikata laifuka; An gurfanar da wasu ƙararraki 415 a kotu; An ceto mutane 46 da aka yi garkuwa da su, an ƙwato makamai 27 da alburusai 115.

Yayin da yake gabatar da mutanen da ake zargin 27 a ranar Juma’a na cikin ‘yan ƙungiyar asiri.

Adesina ya ce, “A ranar 14/12/2024 da misalin ƙarfe 19:30 na safe a lokacin da suke sintiri a yankin Agingi da ke Ƙaramar Hukumar Bassa, jami’anmu sun kama wani mutum mai suna Emmanuel Atu, mai shekara 24 bisa wani zato.

“Lokacin da aka gudanar da bincike mai zurfi kan wanda ake zargin, an samu nasarar ƙwato bindiga guda ɗaya ɗauke da alburusai guda biyar daga hannunsa. A yayin tattaunawar da muka yi da wanda ake zargin, ya amsa cewa shi mamba ne na Ƙungiyar Eiye Black Axe Confraternity( Rukunin masu aikata laifuka).”

Kwamishinan ya ƙara da cewa, “A ranar 15/12/2024 da misalin ƙarfe 08:00 na safe, bayanan da muka samu sun gano ayyukan wasu gungun masu aikata laifi da ake zargin ‘yan bindiga ne da suke amfani da makamai ba bisa ƙa’ida ba a ƙauyen Laplak da ke gundumar Pil-Gani a Ƙaramar hukumar Langtang ta Arewa.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda