An kama mutum 97 yayin zanga-zangar yunwa a Borno
Rundunar ta ce za ta gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum 97 da ake zargi da laifin kisa da ɓarnarta dukiyar jama’a ta miliyoyin Naira, yayin zanga-zangar yunwa a jihar.
A cewar rundunar, an kama mutanen ne a yayin zanga-zangar da aka shafe kwanaki biyu ana yi a Birnin Maiduguri da ƙaramar hukumar Jere.
- APC ta miƙa sunayen ‘yan takararta a zaɓen ƙananan hukumomin Sakkwato
- Kano Pillars na ƙoƙarin gyara kafin sabuwar kaka
Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a Maiduguri, Kwamishinan rundunar, Yusufu Lawal, ya bayyana cewa an ƙwato kayayyaki kimanin guda 91 da suka haɗa da tutocin ƙasar Rasha bakwai da buhunan taki da kayan ofis da dama.
Ya ƙara da cewa yayin da ’yan sanda ke haɗa kai da sauran jami’an tsaro, an kuma ɗauki matakan da suka dace don daƙile tabarbarewar doka da oda a jihar.
Ya ce ɓata-gari, sun yi amfani da zanga-zangar wajen aikata munanan ayyuka da kuma cin amanar ƙasa.
“Baya ga ɓarnatar da dukiyoyin jama’a, wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka haɗa da yara ƙanana, sun kai hari garejin harabar hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar Borno (BOTMA) da ke kan hanyar Baga,” in ji Lawal.
Ya ƙara da cewar: “Daya daga cikin waɗanda ake zargin ya kashe wani direban Keke NAPEP tare da birne gawarsa cikin dare a Maiduguri.”
A cewarsa, sauran mutanen da aka kama sun haɗa da wasu mutum bakwai da suka yi fice a shafukan sada zumunta.
Ya ce an zarge su da rura wutar tarzoma yayin zanga-zangar a jihar.
“Sun kuma riƙa zagin manyan jami’an gwamnati da shugabannin gargajiya da na addini na jihar a shafukan na sada zumunta a yayin zanga-zangar.
“An kuma kama mutum 83 da ake zargi a wurare daban-daban a Maiduguri da laifin lalata kadarorin jama’a tare da cinna wuta da kuma kwashe kayayyak guda 91 a hanyar Baga.”
Ya ƙara da cewa an kuma lalata ma’ajiyar kayan abinci ta hukumar (WFP) ta duniya da cibiyar UNHRC tare da kwashe kayan abinci da kayan ofisoshi.
“Wasu daga cikin waɗanda ake zargin sun kuma fasa gilashin motoci tare da ƙone tayoyi a manyan titunan Maiduguri,” in ji shi.
Sai dai Kwamishinan ya roƙi al’ummar jihar da suke kai rahoton duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma ga jami’an tsaro a jihar.