An kama mutum biyar da ke da hannu a harin bam na Nyanya *Amma shugabanninsu biyu sun tsere

Jami’an tsaro na farin kaya (SSS) sun kama mutum biyar da ake zargin suna da hannu kan harin bam din Nyanya da ke Abuja, inda suka yi alkawarin ba da ladar Naira miliyan 25 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga kama shugabanninsu biyu da suka tsere.Shugabannin, Rufa’i Abubakar Tsiga da […]

An kama mutum biyar da ke da hannu a harin bam na Nyanya *Amma shugabanninsu biyu sun tsere
An kama mutum biyar da ke da hannu a harin bam na Nyanya *Amma shugabanninsu biyu sun tsere

Daga hagu Ahmad Rufa’i Abubakar ne da Muhammad Sani Is’haq da Adamu Yusuf da Ya’u Sa’idu da Anas Isah, wadanda Hukumar SSS ta gabatar bisa zargin suna da hannu a harin bam na NyanyaJami’an tsaro na farin kaya (SSS) sun kama mutum biyar da ake zargin suna da hannu kan harin bam din Nyanya da ke Abuja, inda suka yi alkawarin ba da ladar Naira miliyan 25 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga kama shugabanninsu biyu da suka tsere.
Shugabannin, Rufa’i Abubakar Tsiga da Aminu Sadik Ogwuche da ake zargi da kitsa harin bam din a tashar motocin El-Rufa’i sun tsere kamar yadda kakakin Hukumar SSS Misis Marilyn Ogar ta fadi.
Misis Marilyn Ogar, ta bayyana haka ne a wani taron manema labarai da Kakakin Hedkwatar Tsaro Manjo Janar Chris Olukolade da Kakakin Sojan Najeriya Birgediya Janar Olajide Lalaye da Kakakin ’Yan sanda, CSP Frank Mba suka halarta.
An gabatar da wadanda suka shiga hannu da suka hada da Ahmed Rufa’i Abubakar da Muhammadu Sani Is’hak da Ya’u Sa’idu da Adamu Yusuf da kuma Anas Isah.
Ogar ta ce Rufa’i Abubakar Tsiga da ake wa lakabi da Dokta Tsiga, mutumin Unguwar Gabas, Gidan Mammai, Tsiga ta karamar Hukumar Bakori Jihar Katsina wanda dan Boko Haram ne, shi ya shirya hari bam din, yayin da Aminu Sadik Ogwuche, dalibin harshen Larabci a Jami’ar International Unibersity of Africa da ke Sudan ya taimaka masa.
“A ranar 13 ga Afrilu da daddare Rufa’i Tsiga da Sani Is’hak suka kai mota shake da bama-bamai zuwa tashar Nyanya,” inji Ogar.
Ta ce washegari 14 ga wata da safe Rufa’i Tsiga ya je ya matsa da motar zuwa wurin da ya tayar da bam din.
Shi kuma Sani Ishak da ya fito daga kauyen Balari a karamar Hukumar Ajingi ta Jihar Kano da ya taimaka wa Rufa’i Tsiga wajen daidaita bama-baman yana tsare a hannun SSS tare da sauran mutanen da ke da masaniya kan harin.
Ogar ta ce Aminu Ogwuche wanda aka haifa a Ingila kuma “mai lambar aikin soja, SbC 95/104, ya gudu daga aikin soja ne a shekarar 2006. Kuma ya yi aiki a sashin leken asiri na sojan Najeriya a barikin Child Abenue da barikin Arakan da ke Legas tsakanin shekarar 2001 zuwa 2006, kuma an tura shi Kwalejin NDA a shekarar 2006.
Ta ce an kama shi a ranar 12 ga Nuwamban 2011 a filin jirgin saman Abuja, lokacin da ya dawo daga Ingila bisa zargin hannunsa a ayyukan ta’addanci, amma aka bayar da belinsa ranar 15 ga Oktoban 2012 ga mahaifinsa Kanar Agene Ogwuche (mai ritaya) sakamakon matsin lambar masu rajin kare hakkin dan Adam da suka rika zargin an tauye masa ’yanci.
An kama Ahmed Rufa’i Abubakar da ake wa lakabi da Abu Ibrahim ko Mai-Turare wanda ya fito daga kauyen Yarimawa ta karamar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa ne a ranar 22 ga Afrilu a Gwantu, karamar Hukumar Sanga a Jihar Kaduna, kuma ya Rufa’i Tsiga ya tabbatar masa cewa shi da wasu ’yan Boko Haram ne suka kai harin. A cewar Ahmed Rufa’i, Tsiga ya shaida masa cewa shugaban Boko Haram na kasa ya umarci dukkan ’ya’yan kungiyar su tare a dajin Gaaba (wani sansanin ’yan Boko Haram) don shirye-shiryen kaddamar da hare-hare a kan Najeriya.
Kuma Rufa’i Tsiga ya aika wa Ahmed Rufa’in katin waya na Naira 800 bayan harin, ta amfani da wayar Sani Is’hak, wanda aka kama a kauyen Utako sakamakon bayanin da aka samu daga Ahmed Rufa’i, wanda ya ce Tsiga ya shaida masa an hada bam din ne a gidan wani mai suna Yusuf.
Sani, yaron shago ne a kantin sayar da magani na Rufa’i Tsiga mai suna Kishi Clinic a Utako, kuma nan ne wurin tarukan sirri na Boko Haram a Abuja.
Sani ya ce kwana daya kafin tashin bam din, shi da Tsiga sun tuka motar suka ajiye ta a bayan wasu bas hudu a tashar Nyanya, kuma washegari da safe wajen karfe 7:00 Tsiga ya je ya tada bam din.
Shi kuwa Ya’u Sa’idu da ake kira da kotar Rama an kama shi ne a Tsanyawa da ke Jihar Kano a ranarr 29 ga Afrilu, kuma an ce yana aiki ne a shagon Tsiga na Utako.“Duk da ya musanta kasancewa dan Boko Haram, ya ce kawunsa Tsiga da Sani Is’hak sun yi kokarin ya shiga kungiyar a lokuta da dama,” inji Marilyn Ogar.
Sa’idu ya ce Tsiga da Sani da Ogwuche ne suka shirya harin, kamar yadda jami’an tsaro suka ce, inda ya yi bayanin kai-kawon masu shirya harin kafin da bayansa.
Ya ce lokacin da Tsiga ya samu labarin an kama Sani Ishak sai ya gudu daga Utako, ya bar shagonsa a hannun Sa’idu. Kuma an ce ya aika wa matarsa Hauwa sakon tes cewa ta kwashe nata ya nata ta gudu daga yankin.
Shi kuwa Adamu Yusuf da aka kama a Jihar Bauchi ranar 5 ga Mayu, kuma ya yi ikirarin shi dan Boko Haram ne, malami ne a masallacin Finance kuarters da ke Wuye, Abuja, kuma ya shaida wa jami’an tsaro cewa duk da ya san Rufa’i Tsiga bai sanya hannu a harin bam din ba, amma ya bayyana sunayen ’yan kungiyar da ya sani.
Adamu ya ce Tsiga ya kira shi a ranar da bam din ya tashi, inda ya ce aiki ya yi kyau.
Mutum na biyar Anas Isah wanda dan asalin garin Tsiga ne an kama shi ne ranar 3 ga Mayu a kauyen Unguwar ’Yan Tagwaye da ke karamar Hukumar Faskari, Jihar Katsina. An ce lokacin da ya zo Abuja ya yi tallar Yogut a shekarar 2011 kafin ya kama aiki a wani katin magani a Wuye a shekarar 2012. Anas ya ce a shekarar 2013 ne Tsiga ya nemi ya yi aiki a katin magani a kauyen Utako na wata biyar.
Kuma duk da ya musanta kasancewa dan Boko Haram ya ce Sani Is’hak da Rufa’i Tsiga ’yan kungiyar ne saboda Tsiga ya tabbatar masa shi dan kungiyar ne.

Zanga-zangar ’yan matan Chibok: ’Yan sanda sun gurfanar da wakilin Daily Trust a kotu

Daga John D. Wada, Lafiya

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta gurfanar da wakilinmu na jaridar Daily Trust da ke jihar, Hir Joseph a gaban kotu bayan tsare shi a ranar Juma’ar da ta gabata kan wani rahoto da ya buga game da zanga-zangar a sako ’yan matan Chibok a Lafiya.
Ana tuhumarsa ne da laifin buga labarin karya, kuma ’yan sandan su nemi a tsare shi a kurkuku bisa zargin in aka ba da belinsa zai iya kawo cikas ga binciken da suke yi, tare da kara bayar da irin wannan rahoto.
Takardar bayanin karar da dan sanda mai gabatar da kara a gaban Babban Kotun Majistare Mista D.O Abolarin ya gabatar ta yi zargin cewa Hir Joseph da niyya don bata suna da sanya shakku kan mutuncin ’yan sanda ko don cimma wani burin a kashin kai ya rubuta labarin karya da ke nuna cewa mata ’yan sanda suna adawa da matakin da Gwamnatin Tarayya ko Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ke dauka don ceto ‘’yan mata ’yan makarantar Chibok.
Takardar ta kara da cewa wakilin ya kuma bata martabar Rundunar ’Yan sandan Jihar a cikin rahotonsa inda ya ce rundunar ta tsare ’yan sanda mata shida bisa zargin shiga cikin zanga-zangar ta Lafiya a makon jiya.
Wakilin ya umusanta zarge-zargen lokacin da ya gurfana a gaban alkalin kotun Majistare Yakubu Egga. Kuma lauyoyi sun yi muhawara kan belinsa, inda suka ce laifin da ake zargi ana iya ba da beli a kai.
Lauyoyin wadanda Barista Mohammed danjuma ya jagoranta sun hada da Abubakar Abubakar Dogara da Oshafu Mohammed Zakarai da kuma Mohammed Abdul Ibrahim.
Shugabannin kungiyar Lauyoyi reshen Lafiya a karkashin Barista Ortan Gabriel Akaaka sun halarci kotun tare da lauyoyi wadanda suka tsaya wa wakilin.
Alkalin ya ba da belin wakilin kan Naira dubu 150, ko mai tsaya masa. Kuma Shugaban kungiyar ’Yan Jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Mista Daniel Yakubu ya sanya hannu a matsayin mai tsaya masa don karbar belinsa.
Kotun ta dage ci gaba da zaman shari’ar zuwa 19 ga Yunin mai zuwa.