An kama mutum biyu da fatar jakuna a Jigawa
Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta kama wadansu matasa bisa zarginsu da yin fawan jakuna a kasuwar Maigatari da ke jihar. Matasan masu suna Ayuba Jacob da Henry Dickson ’yan asalin Jihar Filato an kama su ne da fatun jakuna bakwai da suke tarawa domin yin safararsu zuwa Filato a matsayin ganda.Shugaban Hukumar Hisba ta […]
Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta kama wadansu matasa bisa zarginsu da yin fawan jakuna a kasuwar Maigatari da ke jihar. Matasan masu suna Ayuba Jacob da Henry Dickson ’yan asalin Jihar Filato an kama su ne da fatun jakuna bakwai da suke tarawa domin yin safararsu zuwa Filato a matsayin ganda.
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Alhaji Aliyu Galamawa ya ce sun yi bincike a kan wadanda
suka kama kan yaya suke yi da naman jakunan idan sun fede amma sai suka ce suna binnewa ne ba sa sayarwa saboda Jigawa yanki ne na Musulmi.
Ya kara da cewa sun shaida wa hukumarsa cewa ba su taba fede jaki mai rai ba sai dai matacce kuma
mataccen jakin idan sun fede suna binne naman ne su dauki fatar kawai amma ba sa sayar da naman kamar yadda ake zargi ko suna hada baki da mahauta ne suna sayar wa mutane naman.
Alhaji Aliyu Galamawa ya ce duk da bayanan da suka samu a wajen wadanda suke tuhuma jami’ansa na karamar Hukumar Maigatari sun gabatar da su a gaban Kotun Majistare da ke yankin domin yi musu shari’a.
Ya cew alkalin kotun Mai shari’a Sadisu Musa Maigatari ya yanke wa matasan tarar Naira dubu bibbiyu kowannensu ko wata biyu a gidan yari domin hakan ya zama darasi ga sauran jama’a, inda nan take suka biya tarar kuma kotun ta ja kunnensu kan su guji yin haka a nan gaba.