An kama mutum biyu kan kisan wata mata saboda maita
Ya kamata jama’a su fahimci cewa doka ba ta ba mutane damar ɗaukar al’amura a hannunsu ba.

Rundunar ‘yan sandan yankin Biu ta tsare wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wata mata ‘yar shekara 50 da ake zargi da bokanci da maita.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Yusuf Lawan ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Maiduguri.
- Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88
- Yadda ƙananan yara ke zaman kurkuku ba tare an da kai su kotu ba
Kwamishinan ya ce an kashe matar mai suna Hajara Saleh ne a ranar 21 ga watan Fabrairu a unguwar Bantine da ke Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno.
Kwamishinan ya bayyana cewar, waɗanda ake zargin — Ja’o Muhammad da Idris Muhammad — sun yi tarayya wajen kashe matar a dalilin zargin maita da suke mata.
Lawan ya ce matar ta samu raunuka a wuyanta, kafafu, da hannayenta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarta.
Ya ce wani mazaunin unguwar Dadinkowa Gunda ne ya kai wa ’yan sanda rahoton faruwar lamarin da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar.
“Da isa wurin da lamarin ya faru, jami’anmu sun gano cewa mijin nata Saleh Bole da sauran ‘yan uwa sun rigaya sun binne ta kamar yadda addinin musulunci ya tanada,” in ji kwamishinan.
Ya ƙara bayyana cewa, duk da jana’izar da aka yi wa matar amma jami’an ‘yan sanda sun yi nasarar ɗaukar hoton gawar marigayiyar tare da tattara muhimman shaidu.
Kwamishinan ya bayyana abin da ya faru a matsayin dabbanci da rashin gaskiya, yana mai gargaɗin cewa bai kamata a yi amfani da zargin maita a matsayin hujjar tashin hankali ko kisan gilla ba.
“Rundunar ‘yan sanda ta jajirce wajen gurfanar da duk wadanda suka aikata wannan danyen aiki a gaban kuliya.
“Don haka ya kamata jama’a su fahimci cewa doka ba ta ba mutane damar ɗaukar al’amura a hannunsu ba,” inji shi
A cewarsa, waɗanda ake zargin suna fuskantar tuhuma da suka haɗa baki, kisan kai, da sauran laifuka masu alaƙa da su, inda ya ce za a gurfanar da su gaban kuliya da zarar an kammala bincike.
Lawan ya buƙaci al’umma da su kai rahoton zargin bokanci ko duk wasu korafe-korafe ga ‘yan sanda maimakon ɗaukar doka a hannu.