An kama mutum biyu masu tono gawarwaki a makabartun Oyo

Mun kama mutum na farko a lokacin da yake tono wani sabon kabari a wata makabarta a garin Shaki.

An kama mutum biyu masu tono gawarwaki a makabartun Oyo

Amotekun

Asirin wasu mutane biyu ya tonu a lokacin da jami’an Amotekun suka kama su dauke da kokon kawunan dan Adam da ake zargin sun tono daga wata makabarta a garin Shaki a Jihar Oyo.

Kwamandan Rundunar Amotekun a Jihar Oyo, Kanar Olayinka Olayanju mai ritaya ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da Aminiya ta wayar tarho.

A cewar Kanar Olayanju “mutanenmu sun kama mutum na farko ne cikin daren ranar Litinin a lokacin da yake tono wani sabon kabari a wata makabarta a garin Shaki.

“Kuma wannan mutumi da muka titsiye ne ya fada mana sunan maigidansa da ya aiko shi yin wannan aiki.

“Mun kuma samu nasarar kama mai gidan nasa a gidansa da ke Oba Abimbola Layout a garin Shaki,” inji Kanar Olayanju.

Ya bayyana cewa, an samu sabon kokon kawunan mutane guda biyu a tare da wadannan mutane da ba su bata lokaci wajen furtawa da bakinsu cewa sun amince da aikata laifin da ake zarginsu da shi ba.

Kanar Olayanju ya kara da cewa, da zarar sun kammala bincike za su mika mutanen ga ’yan sanda kamar yadda dokar ta tanadar.

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo