An kama mutumin da ya mari matarsa ta mutu
Rundunar ‘yan sandan Legas ta kame wani mutum da tsautsayi ya same shi bayan ya mari matarsa, ta fadi ta mutu nan take. Mai magana da yawun rundunar’yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Larabar da ta gaba ta ne mai Unguwar Atan da ke yankin Sango Ota […]
Rundunar ‘yan sandan Legas ta kame wani mutum da tsautsayi ya same shi bayan ya mari matarsa, ta fadi ta mutu nan take.
Mai magana da yawun rundunar’yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Larabar da ta gaba ta ne mai Unguwar Atan da ke yankin Sango Ota a jihar Ogun Rafiu Gbadomasi ne ya ankarar da ‘yan sanda suka kame mutumin mai suna Kingsley Madukwe mai shekaru 40, dan asalin jihar Anambra da ke sana’ar acaba, ya ce an samu karamar rashin jituwa ne tsakanin Kingsley da matarsa Glory Madukwe mai shekaru 40.
Glory, ta haifa masa ‘ya’ya 8, ya ce matar na da karamin yaro dan shekara daya, “A daren da lamarin ya faru, taron ya yi ta tsala kuka abin da ya sanya Kingsley farkawa daga bacci ya umarci matarsa da ta shayar da yaron nono, ita ko ta ce sam baza ta iya shayar da shi ba domin ta gaji, nan ta tashi ta bar masa yaron ta shiga turaka a daidai lokacin da yaron ke ci gaba da tsala kuka lamarin da ya fusata shi ya wanke ta da mari nan take ta fadi ta mutu.” In ji shi.
DSP Abimbola Oyeyemi, ya ce an kai gawar matar dakin ajiyar gawa ta babban asibitin yankin domin zurfafa bincike, yayin da aka tasa keyar Kingsley zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar inda ake ci gaba da bincikarsa kafin a gurfanar da shi a gaban kotu.