An kama mutumin da ya yi barazanar gayyatar ’yan awaren IPOB zuwa Legas

An nemi kama shi a fadarsa, amma sai ya tsere zuwa wani otal.

An kama mutumin da ya yi barazanar gayyatar ’yan awaren IPOB zuwa Legas

Wasu ’yan awaren Biyafara

Jami’an Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS sun kama jagoran kabilar Igbo mazauna rukunin gidajen Ajao a Legas, Fredrick Nwajagu.

Fredrick Nwajagu ya yi barazanar gayyatar ’yan kungiyar aware ta IPOB zuwa Legas don kwato wa al’ummar Igbo kadarorinsu a jihar.

Bayanai sun bayyana cewa, an kama jagoran Igbo ne da safiyar Asabar a wani samamen hadin gwiwa tsakanin jami’an DSS da ’yan sanda.

Aminiya ta ruwaito cewa, jami’an tsaron sun nemi kama shi a fadarsa, amma sai ya tsere inda suka rika bin sawu har suka kama shi a wani otal.

A cikin wani hoton bidiyo da aka fitar ranar Juma’a a shafin Twitter, Mista Nwajagu mai shekara 49 ya yi barazanar gayyatar ’yan awaren IPOB zuwa Jihar Legas domin kare ’yan kabilar Igbo mazauna jihar daga hare-haren da ya ce ana kai musu.