An kama rabaran da wasu mutum 20 kan zargin sayar da yara
Wani shugaban majami’ar darikar katolika da ke Jihar Akwa Ibom mai suna Rabaran Okono Joseph na cocin Senti Peter a gundumar Owerri tare da wasu mutum 20 sun shiga komar’yan sanda kan zargin sun sayar da wasu yara biyu a kan Naira dubu 900.Sashen kula da masu aikata miyagun dabi’u da sauran laifuka (DSS) a […]

Wani shugaban majami’ar darikar katolika da ke Jihar Akwa Ibom mai suna Rabaran Okono Joseph na cocin Senti Peter a gundumar Owerri tare da wasu mutum 20 sun shiga komar’yan sanda kan zargin sun sayar da wasu yara biyu a kan Naira dubu 900.
Sashen kula da masu aikata miyagun dabi’u da sauran laifuka (DSS) a jihar, sun tabbatar wa manema labarai a Uyo, cewa komarsu ta kama wadancan a makon jiya, inda take zarginsu da cinikin kananan yara da shekarunsu ke tsakanin uku zuwa hudu, kamar yadda Mataimakin shugaba mai kula da jami’an tsaron, Mista Fubarah Duke ya bayyana.
Mista Duke ya shaida wa Aminiya cewa wasu mata biyu, Uche Joel da Canice Onyeka, ’yan asalin Jihar Imo da sauran wadanda ake zargi da suka hada da Mercy Etim, Collins Edet, Caroline Nkwonna, Cecelia Ngene, Eleka Okoye, NwaonuOkoro, AdaobiOnyeka, Elizaberth Onubogu, Umah Ebale, Nwadika, Florence Onyodobi, Emenka Anaefuna, Nnamdi Oguagu, Ifeoma Gladys, NwaezeChinenye, Roseline Idam, bibian Ogbonna da kuma Dabid Ogbuagu, duk suna hannu kuma ana bincikensu.
Mataimakin Darktan ya kara da cewa kimanin sama da yara 60 ne aka sayar a wannan yanki ga masu saye da safara kananan yara a wannan jiha.
Dangane da yadda har dubun wadanda ake zargin ta cika, aka kamasu, Aminiya ta ji mataimakin darakta Duke yana cewa, “korafin yawan samun bacewar yara kanana da kuma saye da sayar da su ta sanya muka dukufa yin bincike, wanda muka fara tun daga Jihar Abiya, makwabciyar jihar nan, har zuwa ta Ebonyi kafin a yi katarin kama wadanda ake zargi dan tsakanin nan, kuma mun kubutar da yara 20 da ake boye da su za a sayar ana jiran masu saye.”.
Game da batun ko me ake yi da yaran idan masu saye sun saye su, sai ya ce, “Ana sanya su aikin gida ne, wasu kuma akan yi kokarin fita da su kasashen ketare ne, masu sayen galibi, kamar yadda muke samun bayani, suna fakewa ne da rashin samun haihuwa, alhali karya ce”.
Jam’an tsaron sun bayyana cewa da zarar sun kammala bincike za su mika wadanda ake tuhumar ga sashen da ya dace domin daukar mataki na gaba.