An kama rakuma takwas dauke da kwalaben giya a Kasuwar Maigatari

Dogarawan Hisba a Jihar Jigawa sun kama wasu rakuma takwas dauke da kwalaban giya a bakin iyakar Najeriya da Nijar ta cikin Kasuwar Duniya da ke karamar Hukumar Maigatari da aka yi kiyasin kudinta zai kai Naira dubu 500.Giyar wadda ake zargin mallakar wani Ibo ne da ke garin Maigatari Hukumar Hisbar ba ta bayyana […]

An kama rakuma takwas dauke da kwalaben giya a Kasuwar Maigatari
An kama rakuma takwas dauke da kwalaben giya a Kasuwar Maigatari

Dogarawan Hisba a Jihar Jigawa sun kama wasu rakuma takwas dauke da kwalaban giya a bakin iyakar Najeriya da Nijar ta cikin Kasuwar Duniya da ke karamar Hukumar Maigatari da aka yi kiyasin kudinta zai kai Naira dubu 500.
Giyar wadda ake zargin mallakar wani Ibo ne da ke garin Maigatari Hukumar Hisbar ba ta bayyana wa Aminiya sunan mai giyar ba.
Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa Malam Ahmad Tamim Roni wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya shaida wa Aminiya cewa an gabatar da rakuman da masu su a gaban kotun Musulunci kuma an raba masu rakuman da rakuman, kuma kotu ta bayar da
umarni a fasa kwalaben giyar.
Malam Ahmad Roni ya ce dogarawan Hisbar sun samu labarin yadda Ibon ke amfani da Buzaye masu kawo kanwa wajen dakon giyar daga kasar Nijar zuwa Najeriya a cikin chali da silikin zuba kanwa da kuma silken fatar shanu.
“Sakamakon bayanan sirri da ’yan Hisbar suka samu daga jama’a ne suka sanya matakan tsaro a bakin iyakar da cikin kasuwa inda Buzayen suke sauke kaya, inda suka samu nasarar kama Buzayen.
Alhaji Ahmad Tamim ya koka game da rashin issasun kudi da hukumar take fama da shi don aiwatar da ayyukanta da kuma karancin alawus da ake biyan jami’an Hisba.
Ya ce tun daga kan kwamanda zuwa dogarin Hisba babu wanda albashinsa ya kai Naira dubu goma a wata saboda mafi yawansu suna yi ne saboda kishin Musulunci.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi