An kama sarauniyar mayu da iyayen gijinta da ke damfarar mutane a Ibadan

Sabuwar rundunar yaki da satar mutane a karkashin jagorancin ASP Usman Dimka da Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina ya kaddamar kwanan baya ta kama mutane 6 da suka karbi kudade fiye da Naira miliyan 800 ta hanyar damfara daga hannun manyan mutane da ’yan siyasa da jami’an tsaro masu neman mulki […]

An kama sarauniyar mayu da iyayen gijinta da ke damfarar mutane a Ibadan
An kama sarauniyar mayu da iyayen gijinta da ke damfarar mutane a Ibadan

Sabuwar rundunar yaki da satar mutane a karkashin jagorancin ASP Usman Dimka da Kwamishinan ’Yan sanda na Jihar Oyo, Muhammad Musa Katsina ya kaddamar kwanan baya ta kama mutane 6 da suka karbi kudade fiye da Naira miliyan 800 ta hanyar damfara daga hannun manyan mutane da ’yan siyasa da jami’an tsaro masu neman mulki da mukamai da kwangiloli da masu neman maganin cututtukan jikin dan Adam.

Binciken ’yan sanda ya nuna cewa ’yan damfarar suna yin amfani da wata mace a cikinsu a matsayin Sarauniyar Fararen Mayu, inda suka yi nasarar samun dimbin kudade a lokuta daban-daban daga hannun irin wadannan mutane masu neman biyan bukatun duniya.
A Juma’ar da ta gabata ce kwamishinan ya jagoranci jami’ansa da ’yan jarida domin nuna masu wani gida a cikin kungurmin dajin da ke kauyen Oloya da ke kusa da birnin Ibadan, a inda ’yan damfarar suke kai mutane cikin dare suna yi masu sihiri da saddabaru da sauraron bayanan damuwar mutanen da daya daga cikinsu yake yi a boye, a matsayin aljani da taimakon Sarauniyar Fararen Mayu; wacce ke fitowa tana rawa da wakokin mu’amala da aljanu, wanda tun farko ’yan korensu suka shirya wa mutane a cikin sirri domin cutarsu.
“Bayan kama wadannan mutane, mun gano gidajen noman kaji guda 2 da aka gina kowanne a kan Naira miliyan 50 da kananan motoci guda 3 masu tsada duka mallakar jagoran ’yan damfarar.” inji kwamishinan, wanda ya jinjina wa dakarun nasa da suka bankado wannan al’amari. Ya ce da zarar sun kammala bincike za su mika mutanen ga kotu domin yanke masu hukumci daidai da laifin da ake zargin sun aikata.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani, jagoran ’yan damfarar mai suna Alhaji Akeem Azeez Olayode dan shekaru 37, ya ce, a shekarun baya da yake gudanar da sana’ar kida da waka ne ya fada hannun wasu mutane da suka damfare shi kudade masu yawa, suka nemi ya shiga cikin kungiyarsu domin dawo masa da kudinsa. Ya ce, tun a wancan lokaci ya amince da shiga cikin kungiyar da suka rika gudanar da danyen aikin nasu tare har zuwa yanzu da dubu ta cika. Sauran mataimakansa da aka kama su tare, kowanne ya furta da bakinsa irin aikin da yake yi domin zolaya da damfarar mutane.
Ita kuwa Sarauniyar Fararen Mayu mai suna Sherifat Gbadamosi ’yar shekaru 50, an umarce ta ne da ta nuna irin aikin da take yi a gaban jama’a, wanda a nan take ta sanya suturu na ban tsoro ta kama yin wakokin mu’amala da aljanu da taka rawa bisa farin kyalle wanda ta ce tsuntsayen jemagu suna fitowa daga cikin gida su tashi sama a duk lokacin da take gudanar da irin wannan aiki a gaban mutanen da suke damfara.
Mutanen da ke zaune a kauyen na Oloya maza da mata da kananan yara sun fito daga cikin gidajensu suna shewa, domin nuna muranarsu ga ’yan sandan da suka bankado wannan gidan matsafa da ’yan damfara da kauyawan suka tabbatar da ganin wucewar kananan motoci da mutane a ciki da cikin tsakar dare. Sun ce ba su san abubuwan da ake aikatawa a cikin gidan ba sai yanzu da asiri ya tonu.