An kama saurayi da budurwar da ake zargi da sayar da jaririnsu don sayen kwaya
Sun sayar da jaririn ne domin sayen miyagun kwayoyi
Kwamitin ka-ta-kwana don yaki da safarar mutane ya kama wani saurayi da budurwarsa da ake zargi da sayar da jaririn da suka haifa domin sayen miyagun kwayoyi.
An kama Anthony Igbinogun, mai shekara 48 da budurwarsa, Joy Umukoro, mai shekara 28 ne tare da wata kawarsu, Precious James mai shekara 26.
Ana dai zargin kawar tasu ce ta yi uwa da makarbiya wajen kulla haramtaccen cinikin ga wani masayi a birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Da take jawabi ga manema labarai a Benin City, babban birnin Jihar Edo, Shugabar sashen bincike na kwamitin, Abigail Ihonre, ta ce an sayar da jaririn ne a kan Naira miliyan daya da dubu 700.
Ta kuma ce yanzu haka bincike ya yi nisa wajen ganin an kwato jaririn tare kuma da kama wanda ya sayi jaririn dan wata daya.
Amma mahaifiyar jaririn ta ce an sayar da shi ne a kan Naira dubu 700, inda aka ba su tsabar kudi Naira dubu 500, sai kuma wanda ya hada su da mai sayar aka ba shi dubu 170, yayin da ragowar ala sayi kwayoyi da su.
Ta ce tun bayan haihuwar jaririn, rayuwa ta yi musu kunci inda ta ce ta nemi kawar tata ta hada ta da mai sayen jaririn inda ta hada su da mutumin na Fatakwal.
Shi ma mahaifin jaririn ya amsa cewa bayan da budurwar tasa ta kawo masa shawarar sayar da jaririn kuma ya amince kuma ciniki ya fada, an ba shi dubu 100,000 daga cikin kudin.