An kama saurayi kan zargin boye budurwa da canja mata addini

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wani matashi bisa zarginsa da laifin boye wata budurwa tare da canja mata addini. Mutumin mai suna Momo, mazaunin Unguwar Shagari Kwatas ana zargin ya boye budurwar mai suna Maimuna Yakubu tsawon wata uku inda har ya canja mata addini dasuna zuwa Mercy.Momo ya shaida wa Aminiya cewa […]

An kama saurayi kan zargin boye budurwa da canja mata addini
An kama saurayi kan zargin boye budurwa da canja mata addini

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta cafke wani matashi bisa zarginsa da laifin boye wata budurwa tare da canja mata addini.

Mutumin mai suna Momo, mazaunin Unguwar Shagari Kwatas ana zargin ya boye budurwar mai suna Maimuna Yakubu tsawon wata uku inda har ya canja mata addini da
suna zuwa Mercy.
Momo ya shaida wa Aminiya cewa shi bai boye budurwar ba haka kuma bai canja mata addini ba. “Ni dai na san ta tsawon lokaci kuma da addininta na Kirista na same ta. Haka kuma abin da ya sa ta je gidana ta zamo tana yawo ne ba ta da wurin zama hakan ya sa ta zo wurina,” inji shi.
A tattaunawarta da Aminiya Maimuna Yakubu wacce ke zaune a layin Gidan Zoo ta ce ba matashin ne ya shigar da ita addinin Kirista ba, ita ce ta shiga da kanta kimanin shekara 10 da suka gabata. “Ba wai lokacin da muka hadu da wannan saurayin na koma
addinin Kirista ba, dama na dade ina gudanar da wannan addini tsawon shekara 10,” inji ta.
Ta ce ta koma addinin Kirista ne sakamakon rashin kulawa daga iyayenta. “Duk da cewa an haife ni a Musulunci amma iyayena ba su nuna min muhimmancin addinin Musulunci ba, ba su sa ni a wata makaranta da zan koyi addinin ba, haka su ma ba su koya min
komai ba. Hakan ya sa na nema wa kaina wani addinin na daban wato Kirista,” inji ta.
Sai dai babbar yayar Maimuna mai suna Halima Yakubu wacce tunda farko ita ta yi karar matashin gaban Hisba ta musanta abin da ’yar uwar tata ta fadi, inda ta ce babu wata kulawa da ba su ba wa ’yar uwar tasu. “Walalhi babu kulawar da ba a ba ta ba, a matsayinta na ’yar uwarmu. Da a hannuna take amma muka neme ta muka rasa sama ko kasa. Dama tunda ba mu gan ta ba sai da muka nemi wannan saurayi amma ya nuna mana cewa bai san inda take ba, har sai a wannan rana da muka yi kararsa gaban hukuma inda aka kamo shi,” inji ta.
Malam Adam Haruna Bayero, shugaban bangaren harkokin da suka shafi ’yan sanda da laifuka a Hukumar Hisba ya ce kasancewar akwai laifin boye mutum da ake zargin matashin da shi a yanzu haka sun mika lamarin ga Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano don zurfafaf bincike tare da gurfanar da su gaban kotu.