An kama saurayi ya saci kamfan mata 14
‘Yan Sanda sun cafke wani saurayi mai shekara 14 da ake zargi da satar kamfan mata 14 a Jihar Ogun. An damke saurayin ne bayan wata mata mai suna Amudalat Opaleye da ke zaune a layin Kano Street a unguwar Ayetoro ta kai karar sa a caji ofis a Karamar Hukumar Yewa ta Arewa. Kakakin […]
‘Yan Sanda sun cafke wani saurayi mai shekara 14 da ake zargi da satar kamfan mata 14 a Jihar Ogun.
An damke saurayin ne bayan wata mata mai suna Amudalat Opaleye da ke zaune a layin Kano Street a unguwar Ayetoro ta kai karar sa a caji ofis a Karamar Hukumar Yewa ta Arewa.
Kakakin ‘Yan Sanda Jihar Ogun, Abimbole Oyeyemi ya ce matar da shaida wa ‘yan sanda cewa saurayin ya saci jiki ya shiga dakinta ya sace matar kamfai, amma aka kama shi dauke da su yana kokarin sulalewa.
“Nan take Baturen ‘Yan Sanda (DPO)na Ayetoro, CSP Mobolaji Jimoh ya tura jami’ansa suka kamo yaron.
“Bayan samun izinin bincike, an gano kamfan mata da aka yi amfani da su guda 14 a cikin dakinsa.
“Matashin ya amsa aikata laifin amma ya ce wani ne ke sa shi ya samo masa su, kuma ana ta kokarin cafko abokin huldar tasa”, inji jami’in.
Oyeyemi ya ce Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Edward Ajogun ya ba da umarnin mika saurayin ga Sashen Bincikin Manyan Laifuka na Rundunar domin zurfafa bincike.