An kama shanun da aka sato daga Zamfara a Abuja
Sashin yaki da satar shanu da sauran manyan laifuffuka a ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, na gudanar da bincike a kan wasu da ake zargi da hannu a satar shanu a jihohin Katsina da Zamfara. Wata majiya a ofishin ta shaida wa Aminiya cewa hakan ya biyo bayan kama wasu shanu da ake […]
Sashin yaki da satar shanu da sauran manyan laifuffuka a ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, na gudanar da bincike a kan wasu da ake zargi da hannu a satar shanu a jihohin Katsina da Zamfara.
Wata majiya a ofishin ta shaida wa Aminiya cewa hakan ya biyo bayan kama wasu shanu da ake zargin na sata ne da aka kawo su Abuja don sayarwa.
Mutumin da ya kawo shanun 23 a Kasuwar Dabbobi ta Abuja da ke Deidei wadanda mafiya yawansu mata ne wasu ma da ciki, tuni aka kama shi tare da wani mahauci a kasuwar da ake zargin yana taimaka masa wajen sayar da shanun ko yanka su.
Babban Jami’in ’Yan sandan Zuba, C.S.P Mahmud M. Umar da ofishinsa ya kama wadanda ake zargin, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Wakilinmu ya zanta da wani babban jami’i a sashin yaki da satar shanun wanda ya ce tuni sun ziyarci jihohin biyu inda suke gudanar da bincike a kan wasu da ake zargi suna da hannu a cikin lamarin.
A zantawarsa da Aminiya, Sarkin Zangon Deidei Alhaji Muhammadu Sada Kusada wanda a kasuwar da yake shugabanci ne aka kai dabbobin, ya ce babban wanda ake zargin da farko ya kawo shanu tara ne zuwa kasuwar, daga bisani ya karo 14.
Ya ce ya samu nasarar sayar da biyar daga cikinsu ko kuma an yanka su a boye ta hannun wani mahauci ba tare da sanin shugabannin kasuwar ba wadanda suka yi tafiya zuwa jihohinsu na asali saboda hada-hadan kasuwar sabuwar shekara.
“Sai dai daga bisani bayan an sanar da mu cewa wani ya kawo shanu mafiya yawansu mata har da masu ciki, mun sanar da jami’an tsaro al’amarin inda suka zo suka kama mahaucin. “Sai dai jin labarin kama mahaucin ke da wuya sai wanda ya kawo shanun ya sulale inda daga bisani ya bayyana da wata takarda da ya ce wani sarki ne a karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara ya rubuta da ke nuna shanun mallakinsa ne,” inji shi. Shugaban ’yan kasuwar ya ce daga nan ne ’yan sanda su ka zo su ka kama mutumin.