An kama shanun sata 12 a kasuwar Oko-Oba
Shugabannin kasuwar shanu ta Oko-Oba sun kama shanu 12 da suke tuhumar na sata ne.Da yake wa taron manema labarai jawabi, sarkin kasuwar, Alhaji Bello dan-Mubaffa ya ce sun kame shanun ne sa’ilin da wata mota mai dauka shanu 15 ta shigo da su cikin kasuwar, kuma suka tuhumi cewa na sata ne.Ya ce abin […]

Shugabannin kasuwar shanu ta Oko-Oba sun kama shanu 12 da suke tuhumar na sata ne.
Da yake wa taron manema labarai jawabi, sarkin kasuwar, Alhaji Bello dan-Mubaffa ya ce sun kame shanun ne sa’ilin da wata mota mai dauka shanu 15 ta shigo da su cikin kasuwar, kuma suka tuhumi cewa na sata ne.
Ya ce abin da ya kai su ga tuhumar cewa shanun sata ne shi ne ganin yanayin shanun, wadanda biyar daga cikinsu suna da ciki, kuma 11 duk karsanoni ne (wato mata matasa masu karfi a jika) da ba kasafai Bafillace zai sayar da su ba.
Sarkin ya ce ganin haka ne sa’ilin da aka kawo su suka nemi direban da ya kawo su domin ya yi musu bayanin inda ya fito da ko kuma ina mai su yake, amma cikin dan kankanen lokaci, sai direban da motarsa suka yi layar zana, aka neme su, kasa ko sama, aka rasa, lamarin da ya kara tabbatar musu cewa shanun na sata ne.
Ya ce, “Har yanzu da nake muku wannan jawabi, ba wanda ya zo ya ce shanun nan nasa ne, bayan kwanaki 6 da tsare su.
Saboda haka za mu ci gaba da tsare shanun da ciyar da su. Mun sanar da ’yan sanda, wadanda suka zo suka ga shanun kuma suka ce mu ci gaba da ajiye su har sai an samu wanda ya zo ya ce nasa ne, ko kuma idan an rasa mai su har na tsawon lokaci, hukuma ta san yadda ta yi da su, sannan a biya wanda ya dauki dawainiyar ciyar da su da lura da su”.
Yayin da manema labarai suka tambayi ko sun saba ganin irin haka, sai ya ce, “Ba shakka ana kawo shanun sata kuma muna kamawa mu mika su ga ’yan sanda. Wannan ba shi ne karo na farko ba, amma shi ne karo na farko da ya dauki tsawon lokaci wani bai zo ya ce nashi ba ne. Za mu ci gsba da ajiyar su har lokacin da hukuma ta waiwaye mu”.