An kama shi da buhu 300 na tabar wiwi

’Yan sandan sun kama wani mutum na buhuna 300 na tabar wiwi a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas. Kakakin rundunar ’yan sandan jahar, Nwonyi Emeka, ya ce jami’an da ke sintiri karkashin sashen leqen asiri na sashen C4i ne suka kama motar da aka makare ta da kayan mayen. Ana zargin mai unguwa da fyade […]

An kama shi da buhu 300 na tabar wiwi

Wani tulin kayan tabar wiwi da Kwastam ta kwace a Legas ranar 2 ga Afrilu, 2021

’Yan sandan sun kama wani mutum na buhuna 300 na tabar wiwi a Fatakwal, babban birnin Jihar Ribas.

Kakakin rundunar ’yan sandan jahar, Nwonyi Emeka, ya ce jami’an da ke sintiri karkashin sashen leqen asiri na sashen C4i ne suka kama motar da aka makare ta da kayan mayen.

Ya ce an yi nasarar kamen ne bayan wata majiya ta tsegunta wa jami’an tsaro da ke sintirin, inda ba tare da bata lokaci ba, suka bi sawun motarf.

Nwobi Emeka ya ci gaba da cewa “Koda direban motar ya fahimci jami’anmu shi suke bi, sai ya nemi ya fita daga motar ya tsere, amma suka yi wa motar zobe suka kama shi

“A binciken da suka gudanar ne suka ga buhuna 300 da ake zargi suna dauke da tabar wiwi, wanda da zarar an gama binciken su kotu za a mika shi.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan