An kama shi da kokunan kan mutum 18
Wani mutumi mai suna Adelani Ayomide dauke da kokon kan mutane guda 18 a cikin katuwar jikar leda garin Ado-Odo, a Jihar Ogun, ya fada hannun ’yan sanda a lokacin suka binciki kayan da ke cikin jikar. Kakakin rundunar, SP Muyiwa Adejobi ya ce Kwamishinan ’yan sanda Ikemefuna Okoye ya bayar da umarnin tura mutumin ga […]

Wani mutumi mai suna Adelani Ayomide dauke da kokon kan mutane guda 18 a cikin katuwar jikar leda garin Ado-Odo, a Jihar Ogun, ya fada hannun ’yan sanda a lokacin suka binciki kayan da ke cikin jikar.
Kakakin rundunar, SP Muyiwa Adejobi ya ce Kwamishinan ’yan sanda Ikemefuna Okoye ya bayar da umarnin tura mutumin ga sashen binciken manyan laifuka (SCID) domin binciken kwakwaf a gano ainihin wurin da ya samo kokon kawunan da abun da yake so ya yi da su da kuma sanin sauran mutanen da ke da hannu wajen mallakarsu.
Har zuwa lokacin rubuta wannan labari, wakilinmu bai samu damar zantawa da mutumin ba, musamman ma da yake ’yan sanda sun ce sai sun kammala bincikensu kafin su kyale ’yan jarida zantawa da shi.
Jihar Ogun ta yi kaurin suna dangane da yawan samun mutane suna tonon kaburbura domin cire wasu abubuwa daga sassan jikin gawa. Rundunar ’yan sandan jihar ta sha kama masu aikata irin wannan aiki da takan gurfanar a kotu, bayan ta kammala bincike.
A daidai wannan lokaci ne rundunar ’yan sandan ta ce ta harbe wasu ’yan fashi da makami su biyu har lahira a lokacin da ta yi musu kwanton-bauna a kusa da garin Shagamu yayin da suke kokarin kwace Naira miliyan 50 daga wani mutum da suka biyo sawunsa daga daya daga cikin jihohin Kudu maso Gabas.
’Yan sandan sun samu labarin barayin ne tun kafin su kai ga kwace kudin, kuma sun yi nasarar kama daya daga cikinsu da raunuka a jikinsa.
Kwamishina Ikemefuna ya nemi jama’a su rika taimaka wa ’yan sanda da labaran da za su kai su ga gano maboyar miyagun mutane a jihar.