An kama shi da kwayar Exol guda 123,000 a Yobe

Masu safarar tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi sun shiga hannu Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Yobe.

An kama shi da kwayar Exol guda 123,000 a Yobe

Wasu daga cikin miyagun kwayoyin da NDLEA ta kama (Tsohuwar ajiya)

Masu safarar tabar wiwi da sauran miyagun kwayoyi sun shiga hannu Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) a Jihar Yobe.

Kakakin hukumar a jihar, Ramatu SB, ta ce an kama fakiti-fakitin kwayar Exol guda 123,500 a hannun daya daga cikinsu ya fito daga Karamar Hukumar Geidam.

Ramatu ta ce, na biyun an kama shi ne da kwayar tramadol guda 5,000 na ukun kuma da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 15.7.

A cewarta, wadanda ake zargin shekarunsu 20 zuwa 32 ne kuma dukkansu jami’an hukumar da ke sintiri a hanyar Gashua zuwa Nguru ne suka cafke su.

A cewar kakakin ta NDLEA, jami’an su sun kuma kama wani wanda ake wa lakabi da Ramos, wanda da kilogiram 94.74 na tabar wiwi.

Ta bayar da tabbacin cewa da zarar sun kammala bincike za a gaurfanar da su a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka kamar yadda doka ta tanada.

Gwamnatin Kano za ta kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

‘Nijeriya ce ƙasa ta 140 mafi rashawa a Duniya’

BUA ya raba wa asibitoci magunguna a Sakkwato

Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya suya sheka daga PDP zuwa APC

Tags